in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kawo cikas ga jarin waje bisa dalilin wai kiyaye tsaron kasar
2018-08-15 19:26:21 cri

Kwanan baya, kasar Amurka ta kaddamar da dokar yin gyare-gyare kan ayyukan zuba jarin waje da nufin kiyaye taron kasa, wannan ne karo na farko da kasar ta sabunta da karfafa ayyukan kwamitin kula da jarin waje a cikin shekaru kusan goma da suka gabata, inda za a yi nazari mai zurfi kan jarin waje da ake zuba wa Amurka.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Amurka ta kan kayyade jarin waje ne bisa wani dalili, wato kiyaye tsaron kasar. Amma, har zuwa yanzu kasar na fifita kan a duniya a fannonin siyasa, tattalin arziki, aikin soja, da kimiyya da fasaha da dai sauransu, babu wata kasa da za ta kalubalanci tsaron kasar ta Amurka. Don haka, ana ganin cewa, kasar Amurka ta dauki wannan mataki ne da nufin hana abokan takararta su samu sabbin fasahohi har su girgiza matsayinta na babakere da kokarin mallakar duniya.

Manazarta sun nuna cewa, matakin kasar Amurka na kayyade jarin waje zai hana ci gaban kamfanonin kasar, da ragewa 'yan kasar guraban ayyukan na wani lokaci, kana kuma zai yi mummunan tasiri kan ci gaban masana'antun kasar da ayyukansu na yin kirkire-kirkire na dogon lokaci. Ya kamata 'yan siyasar kasar su amince cewa, samun sabbin fasahohi bukatun kasuwa ne na yau da kullum na kamfanoni. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China