in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen Turkiya da Rasha sun yi Allah wadai da takunkumin da Amurka take kaddamarwa
2018-08-15 11:12:56 cri

Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Mevlut Çavusoglu, ya gana a jiya Talata, da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavlov, wanda ke ziyarar aiki a Ankara, idan suka yi tir da kakkausar murya kan takunkuman da Amurka take kaddamarwa, tare kuma da nanata wajibcin inganta dangatakarsu bisa manyan tsare-tsare.

Yayin taron manema labarai da aka yi bayan ganawar tasu, Çavusoglu ya bayyana cewa, takunkumin da Amurka take kakabawa Turkiya na kawar da amincin da Amurka ke da shi a idon duniya, yana mai cewa ya kamata a kawo karshen zamanin nuna karfi. Ya kuma jaddada cewa, bunkasuwsar tattalin arzikin Turkiya mai dorewa zai kawo alfanu ga sauran kasashe makwabtaka.

A nasa bangaren, Sergei Lavlov ya nuna gamsuwa sosai ga matakin da Turkiya ke dauka na kin mara baya ga takunkumin da Amurka ke kakabawa Rasha. Ya kuma bayyana takunkuman da Amurka ta sanyawa Turkiya da sauran kasashe a matsayin na rashi imani, wadanda kuma suka sabawa doka, inda ya ce Amurkar na da zummar neman samun rinjaye a cinikin duniya ba bisa adalci ba, matakin da zai kawo illa ga darajar takardar dala a matsayinsa na kudin da ake amfani da shi wajen cinikayya tsakanin kasa da kasa.

Dadin dadawa, ministocin biyu sun tattauna kan halin da kasar Sham ke ciki da nanata tabbatar da dorewar ci gaban da aka samu kan taron Astana game da kasar, tare kuma da kara hadin kansu a wasu yankunan kasar Sham da ke samun sassauci ta fuskar rikici, ciki hadda lardin Idlib. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China