in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin tunawa da 'yan mazan jiya a kasar Zimbabwe
2018-08-14 10:49:17 cri


A jiya Litinin 13 ga wata, dubun-dubatar jama'ar kasar Zimbabwe sun taru a makabartar 'yan mazan jiya dake karkarar birnin Harare, don halartar bikin ranar tunawa da 'yan mazan jiya irinta na 38 da aka gudanar tun bayan da kasar Zimbabwe ta samu 'yancin kai a shekarar 1980. A yayin bikin, jama'a sun nuna girmamawa ga mutanen da suka sadaukar da rayukansu a yunkurin 'yantar da kasar Zimbabwe, gami da al'ummar kasar, daga mulkin mallaka.

A wajen bikin, shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya yi jawabi, yana mai cewa in ba domin 'yan mazan jiya da suka sadaukar da kansu ba, da kasar ta Zimbabwe ba ta kai matsayinta na yanzu ba. Saboda haka ya yi kira ga al'ummar kasar da su karbi nauyin da 'yan mazan jiya suka taba dauka, su yi kokarin gina kasarsu. Ya ce,

"Bisa wannan damar da aka ba ni, ina so in bayyana burina na ganin dukkanmu mun dore da kokarin kare zaman lafiya, da hadin kai, da kuma raya kasarmu. Za mu kare tsaron kasa, 'yancin kai da mulkin kai, wadanda 'yan mazan jiya suka taba fafutukar neman samunsu. Kar mu bar sabanin ra'ayi ya janyo baraka tsakaninmu, ko haifar da kiyayya, har ma a kai ga fadace-fadace. Mu al'umma ce daya, kuma kasa ce daya."

Wannan shi ne karo na farko da Mnangagwa ya fito a gaban jama'a, tun bayan da aka sanar da sakamakon zaben shugabancin kasar a ranar 3 ga wata. Bisa sakamakon da aka gabatar, Mnangagwa ya ci zaben bisa yawan kuri'un da ya samu na kashi 50.8%.

Sai dai a nasa bangare, kawancen da jam'iyyar adawar kasar MDC da sauran wasu jam'iyyu suka kafa, ya ki amincewa da sakamakon zaben, inda suka ce an aikata magudi cikin zaben. Kawancen ya riga ya kai kara ga kotun tsarin mulkin kasar a ranar 10 ga wata, kuma ana sa ran ganin kotun ta yanke hukunci wasu kwanaki 14 bayan da ta karbi karar.

Sai dai a cikin jawabinsa na wannan karo, shugaba Mnangagwa ya ce ta hanyar kada kuri'u, jama'ar kasar Zimbabwe sun gudanar da wani zabe mai 'yanci, da adalci, da imani, inda aka bayyana kome a fili ba tare da rufa-rufa ba. Ya ce,

"Wannan babban zabe ya riga ya wuce, a wannan lokaci ya kamata a mai da cikakken hankali, ga kokarin ciyar da harkokin kasarmu gaba. Yanzu muna fuskantar ayyuka masu wuya a fannin raya kasa, saboda haka ya kamata mu yi hadin kai da juna, da kokarin raya tattalin arziki, da gina gidajenmu. Yayin da ake kokarin raya Zimbabwe, don ta zama wata kasa mai 'yanci, da tsarin dimokuradiyya, da walwala, wadda ta bude kofarta ga kasashen waje, tabbas ne za mu gamu da matsaloli da wahalhalu. Amma duk wadannan matsaloli na dan wani lokaci ne, kuma a karshe za a warware su."

Ta la'akari da yanayin da kasar ke ciki, na kokarin neman samun karuwar tattalin arziki, da ta guraben ayyukan yi, da neman sake zama "kwandon burodi na kudancin Afirka", gami da cimma burin shiga cikin jerin kasashen dake da matsakaicin kudin shiga zuwa shekarar 2030, shugaba Mnangagwa ya yi kira ga al'ummar kasar da su nuna kwarewarsu, ya ce,

"Dukkanmu na da damar zama jarumai a wannan sabon zamanin da muke ciki. Ina fata za mu samu wasu jarumai a fannin raya aikin gona. Haka kuma a sauran sana'o'i. Ga misali: hakar ma'adinai, da yawon shakatawa, da raya masana'antu, da kimiyya da fasaha, gami da fasahohin al'adu, dukkansu na bukatar samun wasu jarumai wadanda za su jagoranci aikin raya su." (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China