in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta yi Allah wadai da harin birnin Amman na kasar Jordan
2018-08-14 09:59:56 cri
Mahukuntan kasar Sudan, sun yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai, kan wata cibiyar binciken ababen hawa dake Fuheis, mai nisan kilomita 20 daga arewa maso yammacin birnin Amman fadar mulkin kasar Jordan, harin da ya hallaka jami'in tsaro daya, ya kuma jikkata wasu jami'an su 6.

Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta yi tir da wannan hari, tana mai bayyana shi da kazamin laifi, wanda ya keta alfarmar rayuwar bil Adama, da kyawawan dabi'u na mutumtaka. Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kuma kunshi sakon ta'aziyya ga iyalan jami'in da ya rasu, da kuma fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

A daya hannun kuma, ta jaddada goyon bayan Sudan ga duk wani mataki na marawa Jordan baya, wajen daukar matakan inganta tsaron kasa, da ba da kariya ga al'ummarta, musamman daga 'yan ta'adda da masu nufin aikata muggan laifuka. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China