in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon ci gaban da aka samu bayan shekaru goma da aka kammala gasar wasannin Olympics ta 2008 a Beijiing
2018-08-13 16:57:28 cri



Nasarar kammala ginin filin wasanni da ma wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na Olympics na shekarar 2008 da aka yi a birnin Beijing, abu ne da ya samar da ci gaba ga birnin Beijing da al'umma da ma gwamnatin kasar Sin baki daya.

Ko yaya gogewar da aka samu za ta taimakawa shirye-shiryen wasannin lokacin hunturu na shekarar 2022 da birnin Bejing zai kuma karbar bakunsinsa?

Wasan wuta mai daukar ido ne ya kawata sararin samaniya da kaloli daban daban. Ga kuma tattakin da aka yi a birnin Beijing daga filin Tian'anmen zuwa filin Bird's Nest domin halartar bikin da ya bayyana sabuwar kasar Sin ga duniya. Shekaru 10 ke nan tun bayan da kasar Sin ta burge duniya da bikin bude wasannin guje-guje da tsalle-tsalle. Gasar wasannin Olympics na shekarar 2008 ya yi kyakkyawan tasiri a kan birnin Beijing da ma kasar baki daya.

Wasanin wuta da bikin mai kayatarwa a filin wasanni na "Bird's Nest", sun sanya Li Jiulin yin ajiyar zuciya. Tun bayan da aka nada shi matsayin babban injiniyan da zai jagoranci ginin filin wasanni na kasa a Beijing lokacin da yake da shekaru 35 a 2003, Li ya mayar da dukkan hankali da lokacinsa ga gagarumin aikin, ba tare da samun isasshen hutu ba.

A cewar Li, a wancan lokacin, babu wanda yake da gogewar aiki mai sarkakiya na ginin irin wannan a kasar Sin, kuma babu wani daga cikin kwararru 'yan kasashen waje da ya yi ammana za su kammala wannan aiki da kan su.

Ya ce, daga watan Satumban 2003 zuwa Agustan 2008, ya yi aiki kusan kullum daga asuba zuwa dare, a wasu lokuta ma, sau daya kacal yake zuwa gida cikin wata guda, duk da cewa gidan ba shi da nisa.

Daga karshe dai, kwalliya ta biya kudin sabulu. Ba kadai wajen gudanar da wasannin Olympic na 2008 filin ya kasance ba, domin har bayan kammala wasannin, filin na ci gaba da yin tasiri.

Shekaru 10 bayan bude filin wasa na "Bird's Nest" a watan Oktoban 2008, sabon ginin na babban birnin kasar Sin, ya karbi baki sama da miliyan 35 daga fadin duniya, sannan an gudanar da taruka daban daban kimanin 600, ciki har da wasannin kwallon kafa na kasa da kasa da wasan zakarun guje guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa ta 2015.

Xiang Jun, babban manajan kula da filin wasan, ya ce filin ya samu ci gaba sosai inda yake samun kudin shigar da ya kai sama da yuan miliyan 250, kimanin dala miliyan 36.7 a kowacce shekara.

A yanzu Li Jiulin ya fara tunkarar wani sabon kalubale a matsayinsa na babban injinyan filin wasan kankara ma "Ice Ribbon" wato wurin da za a gudanar da wasannin lokacin hunturu na Beijing a shekarar 2022. Li Juilin mai shekaru 50 a yanzu, ya ce a yanzu yafi aminta da kansa, saboda gogewa da fasahohin da ya samu daga aikin filin wasa na "Bird's Nest"

Ya ce, ginin filin wasan na Beijing ya bude wani sabon babi ga sana'ar gine-gine ta kasar Sin, kuma ya samar da kirkire-kirkire daban-daban wadanda suka samu ci gaba cikin wadancan shekaru, wanda ya ce za a yi amfani da su a ginin filin wasan kankara.

Yayin da Li Juilin ke tsaka da aiki a shekarar 2008, ma'aikacin masana'antar Shougang Liu Boqiang ya fada cikin tsaka mai wuya.

A kokarin birnin na inganta iskar da ake shaka, a shekarar 2005 sai aka tsayar da ayyukan masana'antar sarrafa karafa da aka kafa tun 1919 a yankin Shijingshan na birnin Beijing, inda aka sauya masa mazauni zuwa Caofeidan dake Hebei.

Kamfanin ya kammala kaura ne a shekarar 2010, kuma sama da ma'aikata 60,000 ciki har da Liu Boqiang ne suka sake matsuguni. Liu ya ce, ya shiga fargaba a wancan lokaci, saboda ya kasa tantance makomarsa da ta Shougang.

Sai dai daga baya, ya amince cewa, sauyin gagarumar dama ce gare shi da ma Shougang. Shekaru 10 bayan kaurar, Shougang, daya daga cikin masana'antu mallakar gwamnatin kasar Sin, ya shiga wani sabon mataki na ci gaba, inda yake sarrafa kayayyaki da manyan fasahohi da kuma inganci tare da samun karuwar bakatun jama'a.

Abun da ya fi ba mutane mamaki shi ne yadda aka sauya gine-ginen masana'antar zuwa wurin wasanni da ajiye kayan tarihi.

Da yake tsokaci kan karewa da amfani da tsoffin masana'antu, shugaban kwamitin tsara wasannin Olypics na kasa da kasa Thomas Bach, ya ce Sinawa ba maganar fatar baki kawai suke yi ba, magana suke yi amma a aikace. Ya ce, tabbatar da dorewar aiki shi suka mayar matsayin jigon tsara wasannin.

Cai Xiulan mai shekaru 82 tsohuwar soja ce da ta sadaukar da lokacinta ga aikin tallafi, inda yanzu take cikin shekaru 17 da farawa. Ta fara aikin ne a 2001 lokacin da aka cika da murnar karban bakuncin wasannin lokacin zafi na 2008. A cewarta, wasannin abu ne da ya shafe kasar Sin da Beijing don haka ya shafe ta.

A matsayinta na wadda ta karanta harshen Ingilishi a jami'a, sai ta fara koyar da mutane harshen domin su taimakawa bakin da za su zo domin wasannin. Kuma ta shafe shekaru 4 tana koyar da sojoji 40. A shekarar 2005 ne kuma aka yi mata rajista a matsayin mai ba da tallafi ga wasannin Olypics na Beijing, inda ta fara koyar da harshen ga al'ummomi daban daban mazaunan birnin na tsawon shekaru 2.

Ta ce, aikin ya ba ta damar kara gane basirar da take da ita tare da cimma burinta na rayuwa. A ganin shekarar 2008 a matsayin shekarar da ta bude kofar ba da tallafi a kasar Sin. domin masu ba da tallafi kimanin miliyan 1.7 ne suka taimakawa nasarar wasannin Olympic na Beijing. Kuma tun daga nan ne kuma aikin ya yi ta samun tagomashi. Shekaru hudu gabanin wasannin lokacin hunturu, sama da masu ba da tallafi miliyan 4 masu rajista ne suka shirya ba da taimako ga wasannin.

Wasannin 2008 ya sauya rayuwar Li Jiulin da Liu Boqiang da Cai Xiulan da ma wasu dubban Sinawa. Nan da shekaru 4 masu zuwa, birnin Beijing zai karbi bakuncin wani gagarumin wasan, kuma al'ummar Sinawa, sun shiryawa karbar wannan bakunci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China