in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin ruwan Libya sun ceto bakin haure 60 a gabar tekun yammacin kasar
2018-08-13 10:38:08 cri

Dakarun tsaron tekun Libya a jiya Lahadi sun samu nasarar ceto 'yan ci rani kimanin 60 a wani kwale kwale na roba a tekun yammacin kasar.

Sojojin ruwan sun sanar da cewa, sun gudanar da aikin ceton ne a garin Surman, mai tazarar kilomita 50 daga babban birnin kasar Tripoli, kuma cikin bakin hauren har da kananan yara 4.

Tun bayan tashin hankalin da ya yi sanadiyyar kifar da gwamnatin tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi a shekarar 2011, kasar Libyan ta kasance a matsayin wata matattarar bakin haure wadanda ke son tsallakawa kasashen Turai ta tekun Mediterranean.

Sauyin yanayi yana daga cikin dalilan dake kara yawaitar bakin hauren dake neman tsallakawa kasashen Turai, musamman ta gabar tekun yammacin kasar Libya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China