in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya ya yi alwashin yaki da rashawa
2018-08-13 10:18:14 cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya jaddada aniyar gwamnatinsa wajen yaki da rashawa da masu bijirewa dokokin kasa, duk da kasancewa yana rasa abokansa da aminansa na kusa.

Kenyatta ya ce, ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen aikin bankado da kuma kwato dukiyar baitul malin kasa da aka wawashe ciki har da filaye.

Ya ce, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai kasar Kenyan ta samu galaba a yakin da take yi da rashawa da kuma take dokokin kasa.

"Na rasa wasu daga cikin abokaina na kusa sakamakon yaki da rashawa. A shirye muke mu rasa wasu abokanmu kuma a kan abin da yake shi ne daidai a wajen Allah," Kenyatta ya furta hakan ne a lokacin da yake gudanar da ibada a cocin Nairobi.

Ya ce, ko kudi ko kuma wata alakar siyasa ba za ta hana bankado masu aikata ba daidai ba a kasar.

"Ya kamata mu gina wata kasa mai kima mai cike da jagorori masu tsoron Allah," Kenyatta ya bayyana, ya kara da cewa, rashawa shi ne ginshikin dake dakile mafarkin kasa, wanda ya hada da samun ingantaccen ilmi, da kiwon lafiya, da abinci mai inganci, da kuma ayyukan yi masu nagarta wadanda mutanen Kenya za su yi alfahari da su.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China