Jaridar New York Times ta ruwaito Chad Bown, wani masanin ilimin tattalin arziki dake aiki a cibiyar nazarin tattalin arzikin kasa da kasa ta Peterson, na cewa, matakan da Amurka take dauka wata alama ce da ke janyo damuwa.
A nashi bangaren, Eswar Prasad, wani shehun malami na jami'ar Cornell, ya ce gwamnatin kasar Amurka ta kan dauki matakin da ya shafi harajin kwastam wajen daidaita sabanin ra'ayi a fannin diplomasiyya. A ganinsa, hakan wani mummunan misali ne dake haddasa fargaba.
Ban da haka, Edward Price, wani tsohon jami'i a lokacin gwamnatin Barack Obama, ya ce matakan da kasar Amurka ta dauka na matsawa sauran kasashe lamba ba za su taimakawa daidaita matsalolin da ake fuskantar ba, maimakon haka jama'ar kasar Amurka su ne za su sha wahalar matakan. (Bello Wang)