An gudanar da wani taron kasa a Liverpool domin tunawa da mambobi kusan 100,000 na kungiyar kwadago ta Sinawa CLC, wadanda gwamnatin Birtaniya ta dauke su aiki a lokacin yakin 1914 zuwa 1918.
Wakilin musammam na Sarauniyar Ingila a Manchester Mark Blundell, ya gabatar da jawabi ga mutanen da suka taro a makabartar Anfield na Liverpool, inda aka binne 5 daga cikin mambobin kungiyar CLC. Mutanen da suka hallara sun hada da manyan jami'an soji da shugabannin al'umma da wakilai daga karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Manchester da kuma mambobin hukumomin kasar Sin a Birtaniya.
Mark Blundell, ya ce 'yan kwadagon sojoji ne fararen hula, wadanda suka cancanci mutuntawa da girmamawa a matsayinsu na dakarun Birtaniya, yana mai cewa sun yi bulaguron dogon zango a fadin nahiyar Turai, karkashin matsanancin yanayi domin taimakawa dakarun Birtaniya dake bakin daga. (Fa'iza Msuatpha)