in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sashen sufurin kasar Sin zai tallafawa hadewar yankunan da shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta shafa
2018-08-10 20:35:59 cri

Sashen sufurin kasar Sin ya fadada tsare tsaren hadin gwiwarsa, ta yadda zai taka rawar gani wajen hade yankunan da shawarar "ziri daya da hanya daya" za ta shafa.

Da yake karin haske game da hakan yayin wani taron manema labarai, shugaban hukumar dake lura da sufurin jiragen sama ta Sin CAAC Zhang Qing, ya ce ya zuwa yanzu, Sin ta riga ta sanya hannu kan yarjeniyoyi da kasashen duniya daban daban a fannin sufurin sama.

Yarjejeniyoyin dai sun shafi kasashe da yankuna 125, cikin su kuwa hadda 62, wadanda shawarar "ziri daya da hanya daya" ta shafa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China