in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Yadda kasar Amurka ta matsawa sauran kasashe lamba a tarihi
2018-08-10 20:14:11 cri
A makon da muke ciki, kasar Amurka ta sanar da karbar karin harajin kwastam da yawansa ya kai kashi 25%, kan kayayyakin kasar Sin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 16. Daga bisani kasar Sin ita ma ta dauki mataki na kara haraji kan kayayyakin kasar Amurka a matsayin wani mataki na mayar da martani.

Idan an yi nazari kan matakin da kasar Amurka ta dauka, za a ga cewa kasar Amurka ta na fakewa da dalilin "daidaita yanayin cinikin da ake ciki na rashin adalci", amma a hakika ta dau matakin ne don matsa wa sauran kasashen da tattalin arzikinsu ke karuwa cikin sauri lamba, ta yadda za ta iya ci gaba da mulkin danniya a duniya.

A tarihin kasar Amurka, ta taba daukar mataki irin wannan ga wasu kasashe 2. Kasa ta farko ita ce kasar USSR, wadda ma'aunin tattalin arzikin ta na GDP ya taba zarce kashi 60% idan an kwatanta da GDPn kasar Amurka. Sa'an nan kasar Amurka ta dauki wasu matakai don hana ci gaban tattalin arzikin USSR. Wadannan matakai tare da sauran kura-kuran da hukumar USSR ta yi, sun sa a karshe kasar ta wargaje. Sa'an nan kasa ta biyu, da Amurka ta taba matsawa lamba ita ce kasar Japan, wadda ita ma ma'aunin GDPn ta ya taba zarce kashi 60% idan an kwatanta da GDPn kasar Amurka. Ganin haka ya sa Amurka ta tilastawa kasar Japan rage fitar da kayayyaki, gami da kara darajar kudin kasar. A karshe, tattalin arzikin kasar Japan ya shiga wani yanayi na tafiyar hawainiya, wanda ya dade a ciki har tsawon shekaru 20.

Ta wadannan misalai, za a iya ganin cewa, kashi 60% na GDPn kasar Amurka tamkar wani layi ne da kasar ta shata. Idan ma'aunin GDP na wata kasa ya zarce wannan layi, to Amurka za ta dau mataki don hana kasar ta kara samun ci gaba. Bisa wannan al'ada ne, kasar Amurka take kokarin saka karin harajin kwastam kan kayayyakin kasar Sin.

Sai dai burin kasar Amurka ba zai cika ba a wannan karo, domin yanayin da kasar Sin ke ciki ya sha bamban da na kasar Japan.

Na farko, kasar Sin tana da dimbin jama'a da suke bukatar kayayyaki daban daban, kana ta kafa dandali na hadin gwiwa iri daban daban, tare da sauran kasashe, ba kamar yadda kasar Japan ta taba dogaro kan fitar da kayayyaki zuwa kasashen Turai da Amurka ba.

Na biyu, kasar Sin na da tsare-tsaren siyasa da na tattalin arziki masu dorewa, wadanda kasar Japan ta rasa a baya.

Na uku, akwai cikakkun tsare-tsaren masana'antu a kasar Sin, wadanda suke taka muhimmiyar rawa a kasuwannin duniya. Wannan yanayi ya sa matakin da kasar Amurka ta dauka kan kasar Sin, ka iya haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin kanta.

Saboda haka za a iya ganin cewa, duk da cewa kasar Amurka ta dauki matakin da ta saba yi don neman hana ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, amma matakinta a wannan karo ba zai yi amfani ba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China