in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasar Sin na nuna kwazo wajen shimfida zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2018-08-10 14:06:20 cri



A taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka ko kuma FOCAC wanda aka yi a watan Disambar shekara ta 2015 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da daga matsayin dangantakar Sin da Afirka daga sabuwar dangantaka bisa manyan tsare-tsare zuwa dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni. Xi ya kuma bullo da wasu manyan shirye-shiryen hadin-gwiwa guda goma da suka shafi fannonin raya masana'antu, da ayyukan gonan zamani, da ababen more rayuwar jama'a, da harkokin kudi, da neman ci gaba ba tare da bata muhalli ba, da saukaka matakan cinikayya da zuba jari, da rage talauci, da kiwon lafiya, da al'adu, da tsaro da zaman lafiya da sauransu. Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da babban taron kolin dandalin FOCAC a watan Satumban bana a birnin Beijing na kasar Sin, za mu rika gabatar muku da wasu bayanai dangane da wadannan shirye-shiryen hadin-gwiwa guda goma. Yau za mu saurari bayanin da Murtala ya hada mana dangane da labarin sojojin Sin dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu.

A watan Nuwambar shekara ta 2017, aka jirbe sojojin wanzar da zaman lafiya na kasar Sin a yankin Juba dake Sudan ta Kudu, wadanda ke gudanar da wasu manyan ayyuka bakwai a karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya, ciki har da bada kariya ga ayarin motocin MDD, da tabbatar da tsaro a kewayen sansanonin 'yan gudun-hijira, da taimakawa 'yan sandan wanzar da zaman lafiya wajen kwashe makamai da sauransu.

Daya daga cikin sojojin kasar Sin dake Sudan ta Kudu, Li Dong ya bayyana ayyukan da yake yi:

"Lokacin da nake gudanar da aikin tabbatar da tsaro, na kan koyarwa takwarorina fasahohin ayyukanmu, don su iya aiki da wuri. Alal misali, na kan koya musu yadda za'a tinkari matsalolin ba-zata ta hanyar da ta ce, bisa ka'idojin MDD. Yayin da muke tinkarar matsaloli, ya kamata mu kwantar da hankalinmu."

Wani sojan wanzar da zaman lafiya na daban daga kasar Sin Lin Xiao ya bayyana cewa:

"Wannan shi ne karon farko da na gudanar da aiki a kasar waje. Wata rana, muna hutawa, ba zato ba tsammani sai muka ji karar harbe-harbe daga sansanin 'yan gudun-hijira. Nan da nan sojojinmu suka isa wurin, gaskiya akwai hadari sosai. Amma a matsayina na jami'in tuntuba, ni kadai da ke jin Turanci, dole ne in je."

Yang Tao, wani sojan kasar Sin ne na daban wanda ke aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu. Yang ya ce, ya dade bai dawo gida kasar Sin ba don murnar bikin bazara tare da iyayensa, wato gagarumin bikin shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta al'ummar Sinawa:

"A yayin bikin, muna sintiri a waje. Mun gamu da wasu yaran wurin, muka kuma koya musu Sinanci, har da yadda ake fadan Barka da Bikin Bazara a Sinanci. Mun turawa iyalinmu wani hoton bidiyo da muka dauka, gaskiya suna kewarmu sosai."

Wani muhimmin aiki na daban da sojojin dake aikin wanzar da zaman lafiya ke yi a Sudan ta Kudu shi ne, kare mata da yara. Wannan ya sa, aka sake jibge wasu sojoji mata na kasar Sin a wajen. Daya daga cikinsu, Hao Ruiting ta bayyana cewa:

"Aikinmu a kowace rana shi ne yin sintiri da sa ido a tasha. Lokacin da muke sintiri, mu kan sanya rigar sulke da hular kwano, yayin da muke gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya na sa'a bakwai a kowace rana."

Yu Peijie ita ma soja ce dake aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu, inda ta ce, lokacin da ta fara aiki a wurin, kowa na kiranta "dan uwa", saboda su sojoji mata ne kamar takwarorinsu maza. Yu ta ce:

"Na tuna karon farko da nake bada kariya ga ayarin motoci, babu bambanci ko kadan tsakaninmu da sojoji maza. A wancan lokaci akwai zafi sosai, mun jike jirgif da gumi, sannan idona da gira da hancina har da gashin kaina duk sun cika da kura. Lokacin da muka ji wani ya ce mu maza ne, gaskiya na ji dadi sosai. Saboda a ganina wannan babban yabon da aka mana."

A watan Satumbar shekara ta 2015, a yayin taron kolin harkokin wanzar da zaman lafiya da MDD ta shirya, shugaba Xi Jinping ya yi alkawarin cewa, kasar Sin za ta kafa wata rundunar wanzar da zaman lafiya mai kunshe da dakaru dubu 8, da horas da ma'aikatan kiyaye zaman lafiya dubu biyu ga kasashe daban-daban, da kuma samar da tallafin dala miliyan dari daya ga kungiyar tarayyar Afirka AU.

Irin kokarin da sojojin dake aikin wanzar da zaman lafiya na kasar Sin suka yi ya samu yabo matuka daga jama'ar kasashen Afirka da dama. Kauyen Nakitun na daya daga cikin wuraren da sojojin dake aikin wanzar da zaman lafiya na kasar Sin dake Sudan ta Kudu ke yin sintiri a kowace rana, kuma akwai gidaje kimanin dari biyar a wurin. Shugaban kauyen, Charles Lado ya bayyana ra'ayinsa game da bambancin yanayin tsaron da ake ciki a kauyen, inda ya ce:

"Kafin zuwan sojojin dake aikin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin wurinmu, yanayin tsaro a kauyenmu ya dada tabarbarewa. Bayan da muka yi shawarwari da tawagar musamman da MDD ta tura zuwa Sudan ta Kudu, ta turo sojojin kasar Sin, yanayin tsaro ya inganta kwarai da gaske a kauyenmu. Yanzu ba mu damuwa da hare-haren 'yan bindiga. Gaskiya muna musu godiya saboda ayyukan da suka yi, muna kuma fatan za su ci gaba da wannan aikin. Mazauna kauyenmu da abokanmu daga kasar Sin muna da dangantaka mai kyau, mun gode musu kwarai da gaske. Mu ma za mu ci gaba da yin kokari don karfafa dankon zumunci gami da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wurinmu."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China