in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yaba da yadda ake shirya zabukan da za a shirya a DRC
2018-08-10 10:44:29 cri

Shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat, ya ce kungiyar ta yaba da irin ci gaban da aka samu game da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin Jamhuriyar demokiradiyar Congo DRC da za a gudanar a ranar 23 ga watan Disamba.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, Moussa Faki ya ce, ya gamsu da gagarumar nasarar da aka cimma a ranar Larabar da ta gabata dangane da shirye-shiryen zabukan kasar.

Faki ya kuma yi maraba da shawarar da shugaban kasar Joseph Kabila ya yanke na martaba kundin tsarin mulkin kasar da ma yarjejeniyar siyasar kasar da aka cimma a jajiberen sabuwar shekara kan dacewar tsayawarsa takarar shugabancin kasar.

A don haka ya yi kira, dukkan masu ruwa da tsaki, da su hada kai, ta yadda za a shirya zabukan da kowa zai yi na'am da su.

A ranar Laraba ne dai aka rufe karbar sunayen 'yan takara a zabukan kasar da a baya aka shirya gudanarwa a ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2017.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China