Masharhanta na ganin cewa, wasu matakan da gwamnatin kasar Amurka ta yanzu ta dauka, suna haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya, wadanda suke zagon kasa ga tattalin arzikin dake farfadowa. Yadda Amurka ta maido da takunkuman da a baya aka janyewa Iran tamkar wata shaida ce ga haka.
Kafin haka, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yi gargadin cewa, tattalin arzikin duniya ka iya shiga cikin mawuyacin hali. Kana a cewar bankin duniya, tsanantar tabarbarewar ciniki za ta yi babbar illa ga cinikin kasa da kasa, irin wanda rikicin hada-hadar kudi na shekarar 2008 ya yi, inda kasashe masu tasowa za su fi jin radadin hakan, ganin yadda suke dogaro kan wasu sassa dake matsayin manya a fannin raya tattalin arzikin duniya.
Hakika matakan da gwamnatin Amurka ta dauka, irinsu janye jiki daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, da tada yakin ciniki, da janye jiki daga yarjejeniyar Paris, da kungiyar UNESCO, dukkansu sun sheda wani yanayin musamman na manufofin diflomasiyyar kasar Amurka, wato "rashin tabbas."
Dangane da lamarin, masu nazarin al'amuran duniya na ganin cewa, manufar kasar Amurka ba ta dace da matsayin kasar na tattalin arziki mafi girma, da babbar kasa mafi tasiri a duniya ba. (Bello Wang)