Ana adana kayayyakin tagulla masu dogon tarihi da yawansu ya kai fiye da dubu 5 a dakin adana kayayyakin tarihi na birnin Tongling, wadanda suka shaida tarihin tagulla mai tsawon shekaru fiye da dubu daya na kasar Sin. Kayan tarihi mafi dadewa dake dakin shi ne kayan da aka kera a daular Shang, da ta Zhou ta kasar Sin. (Zainab)