A jiya ne kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun bayar da labarin cewa, gwamnatin kasar Amurka ba ta dakatar da karin harajin kan kayayyakin na kasar Sin ba. Kuma kara harajin, ya tilastawa matsakaita da kananan kamfanonin shirya rufe ko korar ma'aikata ko yin watsi da sabon shirin ko kara farashin kayayyakinsu.
Jaridar USA Today ta bayana a jiya cewa, burin gwamnatin kasar Amurka a karshe shi ne na ganin sauran kasashen duniya sun rage harajin da suke sanyawa kayayyakinsu da ake shiga kasar Amurka da kyautata kasuwar fitar da kayayyakin Amurka. Masharhanta na ganin cewa, idan rikicin cinikayyar ya ci gaba, kamfanonin kasar Amurka za su fuskanci barazana da batun harajin kwastam zai haifar musu. (Zainab)