Gwamnatin kasar Amurka, ta kara harajin kwastam ga kayayyakin Sin don hana bunkasuwar kasar Sin, da kiyaye matsayinta na farko a duniya, kana akwai wani dalili na daban. Manyan kamfanonin samar da karfe na kasar Amurka sun yi amfani da dalilin tabbatar da tsaron kasa da sa kaimi ga samar da karfe a kasar ta hanyar daga harajin kwastam don taimakawa gwamnatin kasar Amurka wajen kin amincewa da rokon kamfanonin kasar na rage harajin kwastam. An yi nunin cewa, wasu manyan jami'an gwamnatin kasar Amurka suna yin mu'amala sosai tare da sha'anin karfe, alal misali, ministan harkokin ciniki na kasar Amurka ya taba sayen wasu kamfanonin samar da karfe, sai dai ya sayar da su don samun riba.
Kara harajin kwastam ya iya tabbatar da tsaron kasar Amurka ne? Watakila jami'an gwamnatin kasar Amurka ba su tabbata ba, amma sun yi imani cewa, kara harajin kwastam zai kawo moriya gare su. Don haka, ba su yi la'akari da moriyar kamfanoni da masu kashe kudi ba. (Zainab)