in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Alibaba ya kaddamar da wata kyauta don tallafawa 'yan kasuwan da suka yi fice a Afirka
2018-08-09 10:23:18 cri
Shugaban rukunin makeken kamfanin nan na Alibaba na kasar Sin da ya shahara a harkokin cinikayyar yanar gizo Jack Ma Yun ya kaddamar da wata kyauta mai suna Netpreneur, don agazawa shugabannin 'yan kasuwar Afirka da suka yi fice.

Za dai a rika ba da kyautar dala miliyan 10 ne cikin shekaru 10 masu zuwa ga 'yan kasuwar Afirka 100, kuma kyautar za ta mayar da hankali ne kan harkokin kirkire-kirkire a yankunan karkara, samar da aikin yi ga mata da masu kananan sana'o'i.

Mr Ma ya ce ya ba da kyautar ce domin taimakawa matasan 'yan kasuwa daga sassan nahiyar Afirka, wadanda suke kokarin inganta rayuwarsu da ma kawo canjin da zai yi matukar tasiri a cikin al'ummominsu.

Ya ce ya kaddamar da shirin ne a lokacin da ya fara kai ziyara Afirka a shekarar da ta gabata, kuma ya gamsu da kuzari da matasa 'yan kasuwa da ya hadu da su ke nunawa.

Ma ya ce za su hada kai da matasan, wajen ganin sun gina tattalin arziki mai dorewa a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.

Daga shekarar 2019, gidauniyar Jack Ma, za ta rika shirya gasa kowa ce shekara, inda za a zabo mutane 10 daga sassan nahiyar Afirka, domin su nuna kwarewar da dabarunsu na harkokin kasuwanci, inda daga karshe za a zabi wanda zai lashe kyautar dala miliyan 1.

Haka kuma dukkan 'yan takara goman za su karbi kyauta a matsayin jari daga gidauniyar ta Jack Ma, baya ga shiga kungiyar shugabannin 'yan kasuwan Afirka ta Netpreneur, inda za su rika musayar kwarewa da albarkatu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China