in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta karbi karin harajin kwastam kan kayayyakin kasar Amurka
2018-08-08 20:50:04 cri
Bayan da majalisar gudanarwar kasar Sin ta ba shi izini, kwamiti mai kula da harajin kwastam karkashin majalisar, ya sanar a yau Laraba cewa, an yanke shawarar karbar karin kudin harajin kwastam da ya kai kashi 25%, kan wasu kayayyakin kasar Amurka da take shirin fitar da su zuwa kasar Sin, wadanda darajarsu ta kai kimamin dalar Amurka biliyan 16.

An ce za a fara aiwatar da manufar tun daga ranar 23 ga watan da muke ciki.

Dalilin da ya sa kasar Sin ta dauki wannan matakin, a cewar kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, shi ne domin mayar da martani ga mataki irinsa da kasar Amurka za ta dauka kan kasar ta Sin.

Don kare hakkinta da tsarin ciniki da ya shafi bangarori daban daban, dole ne kasar Sin ta dauki wannan matakin. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China