in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan bangarori daban daban na Amurka sun ki amincewa da karin haraji kan kayayyakin da Sin ke shigarwa kasar
2018-08-08 15:58:44 cri
Ofishin wakilan ciniki na kasar Amurka ya sanar a ranar 7 ga wata cewa, za a kara sanyawa kayayyakin Sin da ake shigar da su kasar Amurka da darajarsu ta kai dala biliyan 16 harajin kwastam da kashi 25 cikin dari. Wakilan bangarori daban daban na kasar Amurka, ciki har da kungiyar ciniki ta kasar da kungiyar masana'antun dake kera na'urorin daidaita wutar lantarki ta kasar da kungiyar hadin gwiwa ta sayar da kayayyaki da sauran kungiyoyi, sun ki amincewa da kudurin.

Mataimakin shugaban kula da harkokin kasa da kasa na kungiyar ciniki ta kasar Amurka Myron Brilliant ya bayar da sanarwa a wannan rana cewa, manoma, da masunta da ma'aikata, sun gano harajin kwastam zai kawo illa ga ci gaban tattalin arziki a kasar Amurka a dogon lokaci. A ganinsa, ya kamata Sin da Amurka su koma teburin shawarwari don neman hayoyin warware matsalar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China