in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya ce duk wanda ke kasuwanci da Iran ba shi da damar yi da Amurka
2018-08-08 12:00:01 cri

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce ba za a kyale duk wanda ke huldar kasuwanci da Iran ya yi da Amurka ba.

Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa, an sanyawa Iran takunkumai a hukumance, kuma wadannan takunkuman su ne mafi tsauri da aka taba gani

Ya kuma yi gargadin cewa, duk wanda ke huldar kasuwanci da Iran ba zai yi irinta da Amurka ba, inda a watan Nuwamba, za su karu zuwa sabon mataki.

Wannan na zuwa ne bayan da kashin farko na takunkuman da Amurka ta sanyawa Iran ya fara aiki a jiya Talata.

Wadannan takunkuman sun hada da hana Tehran sayen takardun kudin Amurka, da cinikin zinare da sauran karafa masu daraja, da amfani da graphite da samholo da kwal da wasu manhajoji da ake amfani da su a masana'antu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China