in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yabawa kokarin kasar Sin a wajen bikin bada lambar yabo ga masu kare namun daji na bana
2018-08-08 11:05:33 cri
An gudanar da bikin karrama masu kare namun daji na bana a birnin Cape Town a jiya Talata, inda aka jinjinawa kokarin da kasar Sin ke yi na kare namun daji a nahiyar Afrika.

Gidauniyar Alibaba da hadin gwiwar takwararta ta Paradise, dukkaninsu na kasar Sin da suka jajirce wajen kare namun daji a Afrika ne suka bada lambobin yabon.

Da yake jawabi, Jack Ma, Shugaban rukunin kamfanonin Alibaba, kuma daya daga cikin shugabannin Gidauniyar Paradise, ya yi alkawarin wayar da kan duniya game da bukatar daukar aikin kare namun dajin Afrika a matsayin aikin da ya rataya a wuyan kowa, da kuma samar da burin daidaito tsakanin bil adama da sauran halittu, ta yadda kowacce hukuma za ta zama ta na da alaka da muhallin halittu.

A watan Yulin bana ne gidaunaiyar Alibaba da ta Paradise, suka kaddamar da bikin karrama masu kare namun daji. Za a rika karrama masu kare namun daji 50 a kowacce shekara, inda za a basu kyautar dala 3,000 kowannensu, karkashin wani shiri da zai dauki tsawon shekaru 10.

Afrika ita ce nahiyar da tafi kowacce arzikin namun daji, sai da kuma ta na fuskantar matsalar masu safara ba bisa ka'ida ba. Dabbobi kamar karkanda da goggon biri na dab da karewa. A kowacce shekara, masu kare namun daji da dama ne ke sadaukar da rayukansu wajen yaki da masu safarar dabbobi ba bisa ka'ida ba. A tsakanin 2006 da 2016, akalla masu kare namun daji 1,000 ne suka sadaukar da rayukansu ga aikin kare namun daji. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China