in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An bukaci hukumomin lafiya da su gabatar da bayanai game da alluran ciwon haukan kare
2018-08-08 09:51:06 cri

Hukumar kula da harkokin kiwon lafiya ta kasar Sin (NHC) ta ce, daga yanzu wajibi ne hukumomi da cibiyoyin kula da kiwon lafiya a fadin kasar su samar da hidimomin sanya ido da tattaunawa da mutanen da aka yiwa alluran riga kafin ciwon haukan kare na kamfanin harhada magunguna na Changchun Changsheng Life Sciences Ltd.

Hukumar ta NHC wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ta ce ta dauki wannan mataki ne domin kare lafiyar al'umma da ma 'yancin wadanda aka yiwa alluran riga kafin.

Sanarwar ta ce, kamata ya yi a rika kebe sashen samar da bayanai a kananan asibitocin dake yin alluran riga kafi, a kuma samar da kwararrun ma'aikatan da a ko wane lokaci za su rika amsa tambayoyin jama'a, su kuma rika yiwa wadanda aka yiwa alluran riga kafin gwaji a kai-a kai tare da yi musu magani.

Yanzu haka, wata tawaga da majalisar zartarwar kasar ta kafa, ta fara gudanar da bincike don gano wadanda allurar riga kafin ta yiwa illa. An kuma bukaci a dawo da alluran riga kafin ciwon haukan karen da kamfanin harhada magunguna na Changsheng ya samar a kasuwannin cikin gida da wajen kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China