in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in Sin ya gana da shugabar babban taron MDD
2018-08-07 19:51:00 cri
Wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Yang Jiechi, ya gana da shugabar babban taron MDD na 73, Maria Espinosa a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin a yau Talata.

Yayin ganawar, jami'in kasar Sin ya ce, bisa la'akarin da yanayin da duniyarmu ke ciki, kamata ya yi MDD, da babban taron majalisar su nuna kin amince da ra'ayin yin gaban kai, ta yadda za a samu damar nuna bukatar kafa tsarin tattalin arziki irin na bude kofa, da kare tsarin ciniki da ya kunshi bangarori daban daban.

A nata bangare, Madam Espinosa ta ce MDD za ta tsaya kan manufar cudanyar bangarori da dama, da kara kokarin hadin gwiwa tare da bangaren kasar ta Sin. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China