Manyan kafofin watsa labaru na Amurka da Turai sun yi nuni cewa, ganawar da aka yi a shekaru biyu da suka gabata muhimmin batu ne da ya jawo hankalin jami'in gabatar da kara a kotu ta musamman dake ma'aikatar shari'a da dokoki ta kasar Amurka Robert Mueller a yayin da yake yin bincike kan batun musayar sako a tsakanin Amurka da Rasha.
Yayin da zaben rabin wa'adi na 'yan majalisar dokokin kasar Amurka ke karatowa, kana ake kusan kammala yin bincike game da batun musayar sako a tsakanin Amurka da Rasha, manyan kafofin watsa labaru na kasar Amurka ciki har da jaridar The Washington Post, da CNN, da kamfanin dillancin labaru na The Associated Press sun bayar da labari a ranar 5 ga wata cewa, binciken zai kawo illa ga jami'an dake taimakawa shugaban kasar Amurka, musamman babban dansa da ya tsara da ganawa da lauya 'yar kasar Rasha. (Zainab)