in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kokarin samar da wadata ga manoma da makiyayya a hamadar Kubuqi
2018-08-07 10:56:01 cri

Hamadar Kubuqi tana arewancin birnin Ordos na jihar Mongoliya ta gida dake nan kasar Sin, kwatankwacin fadinta ya kai muraba'in kilomita dubu 18 da dari 6, ita ce babbar hamada ta bakwai a kasar ta Sin, yanzu an cimma burin samar da wadata ga manoma da makiyayya a yankin bayan namijin kokarin da gwamnati da kamfanoni da jama'ar yankin suka yi tare.

Kafin shekaru talatin da suka gabata, ana jin tsoron shiga hamadar Kubuqi, har ana bayyana cewa, duk wanda ya shiga hamadar, tabbas zai mutu ko kuma ya galabaita, a wancan lokaci, manoma da makiyayya a yankin suna fama da mummunan talauci, adadin kudin shigarsu a duk tsawon shekara bai kai kudin Sin yuan 400, kana yawancinsu suna zama ne a cikin karamin dakin maras inganci, idan guguwar kura da kasa ta tashi a lokacin bazara, rairayi ya kan rufe dakinsu, har ba su iya bude kofar gidansu ba. Saboda manoma da makiyayya suna zaune a kan hamada ne, a don haka idan za su je garuruwan dake da nisan kilomota 100 domin gudanar da harkokin da suke bukata, dole ne su hau rakumi mai tafiyar hawainiya, shi ya sa suna bukatar kwanaki a kalla shida a kan hanya.

Kwanakin baya ne, wakilanmu suka je hamadar Kubuqi, inda suka ziyarci manoma da makiyayya a yankin domin jin ta bakinsu, a yayin ziyararsu, sun ga manyan sauye-sauyen da suka faru a wurin, ko ina ana ganin ciyayi kore-shar a kan hamadar, haka kuma sun ga hanyar mota mai inganci da aka gina.

A sabon kauyen makiyayya na Daotugacha da kamfanonin suka gina cikin hadin gwiwa karkashin jagorancin gwamnatin yankin a shekarar 2006, an ga itatuwa masu launin kore cikin layi, makiyayya suna zaman rayuwa a cikin sabbin dakunan gidajen kwana, har an ga motoci da dama a bakin kofar gidajen, babu rakumi ko daya, saboda suna yawo ne a ni'imtaccen wurin da aka kebe domin masu yawon shakatawa.

Yanzu adadin kudin shiga na kowanen iyalin kauyen a duk shekara ya kai kudin Sin yuan dubu 120, Sirenbabu, mai shekaru 40 da haihuwa, ya kafa masaukin baki a gidansa, kuma ya dasa ciyayi tare kuma da kiwon sa da tumaki domin kara samun kudin shiga, yana mai cewa, "Ina samu yawancin kudin shiga ne daga masaukin bakin da na kafa a gidana, kana na shirya wasu ayyukan wasa a filin rairayi, da kuma ruwa, gaba daya adadin kudin shigar da na samu ya kai kusan yuan dubu 140 a ko wace shekara."

Gao Maohu, manomin kauyen Hangjinnaoer ya yi suna a yankin ne saboda ya samu wadata kafin takwarorinsu, amma shekaru 20 ko 30 da suka wuce, iyalansa ba su da isasshen abinci da sutura, daga baya ya fara dasa itatuwa, kawo yanzu fadin wurin da ya dasa itatuwa ya zarta hekta 6600, a cewarsa: "Sakamakon goyon bayan gwamnatin yankin, wasu kamfanoni sun zuba mana jari, a don haka na yi kokarin dasa itatuwa da maganin gargajiyar kasar Sin mai suna Licorice a hamada, a baya muna fama da mummunan talauci, amma yanzu mun kubuta daga talauci mun samu wadata."

Gao Maohu shi ma yana aiki ne a rukunin Yili wanda ke gudanar da aikin sarrafa rairayi a Kubuqi, tun daga shekarar 2004, kamfanin ya sa kaimi ga manoman yankin da su kafa kungiyar manoma masu aikin sarrafa rairayi, wato manoman suna kokarin shawo kan barazanar guguwar kura da kasa, tare kuma da dasa itatuwa domin dakile matsalar kafin lokaci. Shugaban rukunin Yili Wang Wenbiao ya bayyana cewa, "Manoma da makiyaya ne suke aiki a cikin rukuninmu, baya samun kudin shiga a kamfaninmu, suna kuma iya kyautata yanayin rayuwarsu ta hanyar dasa itatuwa, saboda haka sun nuna kwazo da himma kan aiki."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, har kullum gwamnatin kasar Sin da karamar gwamnatin yankin suna mai da hankali matuka kan aikin gina halittu masu rai da marasa rai, musamman ma tun daga shekarar 2012, wato bayan da aka kammala babban taron wakilan JKS karo na 18, birnin Ordos yana kara ba da muhimmanci kan aikin, har adadin jarin da aka zuba kan aikin ya kai yuan biliyan 19.1 tsakanin shekarar 2011 zuwa ta 2015, darektan kwamitin JKS na birnin Niu Junyan yana mai cewa, "Muna nacewa ga manufar samar da wadata ga al'ummar yankin ta hanyar gina halittu masu rai da marasa rai, muna kokarin yaki da talauci yayin da muke kokarin sarrafa rairayi, da haka al'ummar yankinmu suna iya cimma burin samun wadata tare kuma da kyautata yanayin rayuwarsu."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China