in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta hukunta marasa gaskiya
2018-08-07 10:48:31 cri

Wata sanarwa da hukumar kula da da'a da raya al'adu ta kasar Sin ta fitar na nuna cewa, an kaddamar da wani kamfel a baya-bayan nan da nufin hukunta masu karya doka ko halayen da ba su dace ba. An dai dauki wannan mataki ne saboda rashin da'ar dake faruwa a bangarorin tattalin arziki da jin dadin jama'a.

Sanarwar ta kara da cewa, kamfel din zai mayar da hankali ne kan matsalolin da suka shafi harkokin sadarwa da zamba ta Intanet, da coge a ayyukan kawar da talauci, da satar jarrabawa ko takardun karya da ake wallafawa a jaridu, zamba a wuraren aiki, da amfani da magungunan kara kuzari a harkokin wasanni da sauransu.

Baya ga kamfel din, kasar Sin tana kuma shirin kaddamar da wani tsari na hukunci da sakawa masu kwazo nan da shekarar 2020, a wani mataki na samar da yanayin rayuwar jama'a mai inganci da yayata mutunci a cikin kasar.

Hukumar ta ce, ya kamata a kara zage damtse wajen kafa tsarin a dukkan fannoni, a kuma kafa irin wannan tsari da zai shafi daukacin al'umma da inganta matakan wayar da kan jama'a game da wannan tsari. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China