in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An buga littafin "Yawo a Afrika" don nuna ci gaban hadin kan Sin da Afrika
2018-08-06 13:20:41 cri

Gidan rediyon kasar Sin CRI ya buga littafin "Yawo a Afrika" a kwanan nan don maraba da taron koli na Beijing na dandalin tattaunwar hadin kan Sin da Afrika da za a yi a watan Satumba mai zuwa. Littafin dai da ya kunshi labaran wakilan CRI kan aikinsu da zamansu a Afirka, ya nuna dankon zumunci da ke tsakanin jama'ar bangarorin biyu da ma sakamakon hadin kansu.

Marubuta 14 na littafin su wakilan CRI ne da suke aiki ko suka taba aiki a Afrika, wadanda suka fahimta sosai kan yadda Sin da Afrika suke bunkasa dangantakar abota a tsakaninsu a dukkanin fannoni bisa manyan tsare-tsare, kuma suna kaunar nahiyar Afrika kwarai da gaske. Bisa kalmomin da suka rubuta da kuma hotuna da suka dauka, wakilan sun bayyana abin da suka ji da suka gani, da ma wadanda suka burge su a yayin ziyararsu a kasashen Afirka, wadanda suka hada da Zimbabwe, Kenya, Najeriya, Masar, Tanzaniya, Zambiya, Afrika ta kudu, Mauritius, Sudan ta kudu, Laberiya, Malawi, Jamhuriyar Kongo, Mozambique, Equatorial Guinea, Botswana, Ruwanda, Mauritaniya, Djibouti, Somaliya, Swaziland da dai sauransu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China