Raya birnin Shanghai don ya zama wata cibiyar hada-hadar kudi a kasuwannin duniya ya kasance wata babbar manufar kasar Sin. Don tabbatar da fifikon birnin a fannin hada-hadar kudi, an tsara matakan da za a dauka da taswirar da za a bi. A cewar Guo Yu, wani jami'i mai kula da harkar tattalin arziki a kwamiti mai kula da ayyukan ci gaba da gyare-gyare na birnin Shanghai, ana kokarin aiwatar da matakan da aka tsara ana kuma samun sakamako mai gamsarwa.
A farkon watanni 6 na bana, an kulla yarjeniyoyin kara zuba jari a birnin Shanghai na dalar Amurka biliyan 21.5, jimilar da ta karu da kashi 18.1% bisa makamancin lokacin bara. Haka zalika, manyan kamfanonin kasa da kasa sun kara bude wasu rassansu 17 a birnin cikin wannan shekara, wadanda suka kasance helkwatoci masu kula da ayyukan sayayya, da nazarin harkoki, da sarrafa kudi, da dai sauransu. (Bello Wang)