Tun daga yau Lahadi, mafi yawan yankunan kudancin Yangtze River, Liaoning, Hebei, Shandong, Shaanxi, Sichuan, Guangdong da kuma yankin Xinjiang za'a samu karuwar zafi wanda zai iya kaiwa maki 35-36 a ma'aunin Celsius, in ji hukumar ta NMC.
Wasu yankunan ma yanayin zai karu zuwa maki 39 a ma'aunin Celsius.
Cibiyar hasashen yanayin tana shawaratar jama'ar dake zaune a yankunan da abin ya shafa da su dauki matakan kariya daga matsanancin zafin da kuma wuta, matakan da suka hada da kaucewa wasu harkoki na yau da kullum da za su iya jefa rayuwarsu cikin hadari. (Ahmad Fagam)