in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: An kasa daidaita sabanin ra'ayi dake tsakanin Amurka da Turai
2018-08-03 16:23:52 cri
Bayan da Donald Trump ya kama aiki a matsayin shugaban Amurka, yana ta kokarin aiwatar da matakai na kashin kai, inda ya mai da hankali kan moriyar kasar Amurka kawai, da lalata tsare-tsaren hadin gwiwar kasa da kasa, ta yadda aka canza huldar gargajiya dake tsakanin Amurka din da nahiyar Turai.

Idan an yi nazari kan ra'ayin da Donald Trump ya dauka wajen hulda da nahiyar Turai, za a ga cewa, da farko, ya raina tsarin hadin gwiwar kasashen Turai, da tunzura wasu kasashe da su janye jikinsu daga kungiyar kawancen Turai ta EU. Na biyu kuwa, shugaba Trump na tsammanin cewa kasashen Turai ba su biya kudi sosai ba, amma suna zama karkashin kariyar da sojojin kasar Amurka suke bayarwa, lamarin da ya sabawa manufarsa, domin baya son ganin Amurka ta ware kudi da yawa wajen taimakawa saura. Saboda haka, ya tilastawa kasashen Turai kara daukar nauyin biyan kudin da kungiyar tsaro ta NATO ke bukata.

Karkashin wannan yanayi ne, mambobin kungiyar EU suka dade suna jin radadin manufar gwamnatin Trump, abin da ya sa suke fushi da kuma sanyin gwiwa, inda suka rasa imanin da aka taba dorawa kasar Amurka. Kafofin watsa labarai na kasashen Turai su ma sun zargi kasar Amurka da kokarin haifar da matsala a "gida", ganin yadda kasar take kallon abokanta a nahiyar Turai, a matsayin "wadanda suka kasa biyan bashi, da 'yan kasuwa da ba su da gaskiya".

A wani bangare kuma, a karkashin tunanin mai da Turai a matsayin abokiyar gaba da Trump ya yi, sanawar hadin kan da shugaban EU Mista Jean-Claude Juncker ya kulla tare da Trump, tamkar wani kyakkyawan fata ne kawai, wanda ba shi da amfani ko kadan wajen daidaita dangantakar dake tsakaninsu, wadda tushenta ya tabarbare sosai.

EU a cikin kungiyarta, bangarori daban-daban na da bambancin ra'ayi kan yarjejeniyar, saboda ganin EU ta bi cikin tsanaki sosai wajen kafa wata doka, sanarwar kuma ba ta warware takaddamar da ta auku tsakanin EU da Amurka ba, balle gabatar da wani daftarin daidaita matsalolin da za su bullo nan gaba.

Wani abu mai muhimmanci a gaban kowa shi ne, Trump mutum ne mai canjawa, kamar matakan da ya kan dauka a fannin ayyukan diflomasiyya, ba su da isasshiyar amincewa ga nahiyar Turai. Bambancin ra'ayi tsakanin Amurka da Turai irin na tsari ne a fannin tsaro, daidaita harkokin duniya, ikon mallakar tattalin arziki da sauransu, ko kadan ba za a iya magance su karkashin mulkin Trump ba. (Bello/Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China