in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cika shekaru goma da kaddamar da layin dogo mai saurin tafiya tsakanin Beijing da Tianjin
2018-08-02 13:16:23 cri


 

Ranar 1 ga watan Agusta, rana ce ta cika shekaru goma da kaddamar da layin dogo mai saurin tafiya da ya hada biranen Beijing da Tianjin, wanda saurin tafiyarsa zai kai kilomita 350 a sa'a guda. A wadannan shekaru, jimillar adadin yawan fasinjojin da suka yi zirga-zirga a cikin layin dogon ta kai miliyan 250. Ba sauya zaman rayuwar mazauna biranen biyu kadai layin dogon ya yi ba, har ma da taimakawa sosai ga bunkasuwar wasu sana'o'i da dama a Beijing da Tianjin gami da lardin Hebei.

Da misalin karfe tara na safiyar ranar 1 ga watan Agusta, a cikin jirgin kasa mai lambar C2211 wanda ya tashi daga tashar jiragen kasa dake kudancin Beijing zuwa tashar Wuqing ta birnin Tianjin, wata 'yar Beijing mai suna Ba ta ce, layin dogo tsakanin biranen biyu ya kawo mata sauki sosai wajen yin bulaguro. Ba ta ce:

"Zan je yawon shakatawa a Wuqing, can kuma zan je Tianjin, tare da kanwata. Za mu yini a can mu dawo an jima da dare. Mun yanke shawarar zuwa Tianjin ne jiya, yanzu muna kan hanya, saboda jirgin kasa na da saurin gaske."

Bayan kaddamar da layin dogon a shekara ta 2008, rabin sa'a kadai ake bukata wajen tafiya tsakanin biranen Beijing da Tianjin, al'amarin da ya rage tazarar dake tsakaninsu, har sauya ayyuka gami da zaman rayuwar mazauna biranen biyu. Mista Li, wani mazaunin birnin Beijng ne, wanda ke kaiwa da dawowa a kowane sati tsakanin Beijing da Tianjin saboda aiki, inda ya ce:

"A baya na kan kashe lokuta da dama wajen zirga-zirga tsakanin Beijing da Tianjian, kamar awa biyu da wani abu daga Beijing zuwa Tianjin. Amma bayan kaddamar da layin dogon, akwai sauri sosai har na yi tsimin sulusanin lokacin tafiye-tafiye. Ina jin dadin tafiya a cikin jirgin kasan."

Bisa alkaluman da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta kasar Sin ta bayar, a cikin shekaru goman da suka gabata, adadin yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta layin dogo mai saurin tafiya tsakanin Beijing da Tianjin ya kai miliyan 250.

 

A dayan bangaren kuma, zirga-zirgar jiragen kasa masu saurin tafiya tsakanin biranen Beijing da Tianjin na raya tattalin arziki gami da kyautata zaman rayuwar al'ummar wurin. Yankin Wuqing na birnin Tianjin na tsakiyar biranen Beijing da Tianjin. A cikin shekaru goman da suka gabata, matsakaicin adadin yawan fasinjojin da suka yi tafiya a tashar Wuqing a kowace rana ya karu daga 366 na shekarar 2008 zuwa sama da dubu goma a yanzu. Kana kuma, jimillar yawan tattalin arzikin wurin ya karu daga kudin Sin Yuan biliyan 16.5 na shekara ta 2008 zuwa biliyan 116.1 a shekara ta 2017. A nata bangaren, darektar cibiyar kula da hidimomin yawon bude ido ta yankin Wuqing, Tao Jingyan ta ce, layin dogo tsakanin Beijing da Tianjin na taimakawa sosai wajen habaka sana'ar yawon bude ido a wurin, inda ta ce:

"Sakamakon zirga-zirgar jiragen kasa masu saurin tafiya tsakanin Beijing da Tianjin, adadin yawan fasinjoji na karuwa sosai, kuma layin dogon na tallata wurinmu. A shekara ta 2012, yawan mutanen da suka zo yankin Wuqing yawon bude ido bai kai miliyan biyu ba, amma zuwa karshen shekarar 2017, adadin ya karu har ya kai miliyan 18.8. A waje daya kuma, jimillar kudin shigar da muka samu daga sana'ar yawon shakatawa a yankin Wuqing ya karu daga Yuan kasa da miliyan dari daya a shekara ta 2012 har zuwa Yuan biliyan tara a bara"

Tun daga ranar 1 ga watan Agustar bana, an canja dukkanin jiragen kasa dake tafiya a layin dogo tsakanin Beijing da Tianjin zuwa na samfurin "Fuxing". Li Xiaodong, wanda ya tuka jirgin kasa mai saurin tafiya na farko daga Beijing zuwa Tianjin a shekaru goman da suka gabata, ya bayyana cewa, layin dogo tsakanin Beijing da Tianjin babbar alama ce ga saurin bunkasuwar jiragen kasa masu saurin tafiya a kasar Sin.  Li ya ce:

"Muna iya cewa, a shekaru goman da suka gabata, sana'ar shimfida layukan dogo masu saurin tafiya a kasar Sin ta samo asali ne daga layin dogo mai saurin tafiya tsakanin Beijing da Tianjin, abun da ya aza tubali mai inganci ga bunkasuwar layukan dogo masu saurin tafiya a kasar Sin da ma sauran sassan duniya. Darussan da muka koya daga zirga-zirgar jiragen kasa masu saurin tafiya tsakanin Beijing da Tianjin, da ayyukan horas da matukan jiragen kasan da na tsara fasinjojin, dukkansu na taka muhimmiyar rawa ga bunkasuwar jiragen kasa masu saurin tafiya na kasar Sin." (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China