in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya zai tafi hutu London
2018-08-02 10:53:00 cri
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, zai tafi hutu birnin London a gobe Juma'a.

Kakakin shugaban kasar Femi Adeshina, ya ce shugaba Buhari zai shafe kwanaki 10 yana hutun.

Ya ce shugaban kasar ya mika wasika ga majalisun dokokin kasar, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. Haka kuma, ya ba mataimakinsa damar rike ragamar shugabancin kasar a madadinsa.

Ko a ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata, shugaban ya yi wata gajeriyar tafiya zuwa birnin London domin duba lafiyarsa. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China