in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 3 sun mutu sanadiyyar rikicin bayan zabe a Zimbabwe
2018-08-02 10:50:40 cri
Mutane 3 sun mutu, wasu gommai kuma sun jikkata, sanadiyyar arangamar da aka yi jiya Laraba, tsakanin masu goyon bayan jam'iyyar adawa da jami'an tsaro a birnin Harare na kasar Zimbabwe.

Kakakin 'yan sandan kasar Charity Charamba, ta tabbatar da mutuwar da ya auku sanadiyyar rikicin da ya kai ga lalata wasu dukiyoyi.

Ta kuma gargadi shugabannin jam'iyyar kawance ta 'yan adawa wato MDC game da ingiza magoya bayansu don su tada rikici.

Gomman magoya bayan bangaren adawa ne suka fita kan titunan Harare domin nuna adawa da jinkirin sanar da sakamakon zaben shugaban kasa, suna masu zargin an tafka magudi.

A nasa bangaren, Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa, ya yi kira ga al'ummar kasar su kwantar da hankali yayin da kasar ke dakon sakamakon zaben.

Ya kuma dora laifin haddasa rikicin kan shugabannin jam'iyyar MDC.

Shi kuwa Nkululeka Sibanda, kakakin dan takarar shugaban kasa na MDC Nelson Chamisa, cewa ya yi, jam'iyyar bata ji dadin asarar rayukan da aka yi yayin zanga-zangar ba, ya na mai zargin jami'an tsaron da amfani da karfi fiye da kima wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

A ranar Talata ne Nelson Chamisa ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben na shugaban kasa, inda ya ce jam'iyyarsa ba za ta amince da sakamakon da ya sabawa hakan ba.

Hukumar zaben kasar Zimbabwe dai ta ce a sa ran samun sakamakon zaben a ranar 4 ga watan nan.

A cewar sakamakon da hukumar ta fitar, jam'iyyar ZANU-PF mai mulki ce ta ci galibin kujerun majalisar dokokin kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China