in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Turkiyya ta lashi takobin mayarwa Amurka martani
2018-08-02 10:47:31 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ya ce mahukuntan kasar za su mayarwa Amurka martani, bayan da Amurkan ta zargi Turkiyya da kame wani fasto Ba'amurke, bisa zargin sa da aikata laifuka masu nasaba da ta'addanci.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta yi tir da matakin da baitulmalin Amurka ya dauka na kakabawa kasar takunkumi, tana mai fatan zai sauya matsaya game da batun takunkumin.

Ma'aikatar ta ce ko shakka babu, takunkumin wata alama ce dake nuna rashin martabawa ga tsarin siyasar Turkiyya, matakin da ka iya gurgunta alakar Turkiyyar da Amurka, kana zai illata yunkurin da ake yi na kawo karshen takaddamar da sassan biyu ke fuskanta.

A ranar Laraba ne dai ofishin baitulmalin Amurka ya zargi ministan shari'ar Turkiyya Abdulhamit Gul, da ministan harkokin cikin gidan kasar Suleyman Soylu da hannu, wajen damke tare da tsare fasto Andrew Brunson.

Kafin hakan, wata kotun kasar Turkiyyar ta yi watsi da kiraye kirayen da ake yi mata, game da soke daurin talala da aka yiwa Brunson. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China