A kakar shekarun baya bayan nan farashin waken soya a CBOT ya samu karuwa, sai dai kuma takaddamar cinikayya tsakanin Sin da Amurka, ta sabbaba saukar farashin sa, a gabar da gwamnatin shugaba Trump na Amurka ke barazanar kara yawan harajin da take karba daga hajojin kasar Sin dake shiga Amurka.
A daya bangaren kuma, farashin alkama a CBOT na ci gaba da karuwa, yayin da yawansa a kasuwa ke yin kasa, kana karuwar yanayin zafi a kasashen dake samar da shi kamar Faransa, da Jamus, da Rasha da Australia ta haifar da karancin sa.
Har ila yau farashin masara ya yi kasa bayan hauhawar da ya yi a kakar amfanin gona 5 a jere. (Saminu Alhassan)