in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fashewar boma-bomai ta hallaka mutane sama da hamsin a Afghanistan
2018-08-01 16:22:55 cri
Jiya Talata, an yi fashewar boma-bomai hau sau biyu a kasar Afghanistan, al'amarin da ya hallaka mutane sama da hamsin.

Da sanyin safiyar jiya, a yankin Bala Buluk na jihar Farah dake yammacin Afghanistan, an kai harin bom kan wata mota wadda ke hanyarta daga jihar Herat zuwa Kabul, fadar mulkin kasar, abun da ya hallaka mutane 11 tare da raunata wasu 31, ciki har da mata da yara da dama.

A ranar kuma, a Jalalabad, fadar mulkin jihar Nangarhar dake gabashin kasar, wasu 'yan bindiga sun kai harin kunar bakin wake, daga baya suka yi musanyar wuta da 'yan sandan wurin, lamarin da ya kashe mutane akalla hudu da raunata wasu takwas, ciki har da 'yan sandan biyu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China