in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar kasar Sin dake MDD ta shirya liyafar murnar cika shekaru 91 da kafa rundunar sojan 'yantar da jama'ar kasar
2018-08-01 11:26:46 cri
Jiya Talata, tawagar dindindin ta kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, ta shirya wata liyafa don murnar cika shekaru 91 da kafa rundunar sojan 'yantar da jama'ar kasar Sin.

Jakadan kasar Sin dake MDD Ma Zhaoxu, da wasu mataimakan babban magatakardan MDD Jean-Pierre Francois Renaud Lacroix da Atul Khare, da Peter Thomas Drennan, gami da mai bada shawara ga babban magatakardan MDD ta fannin soja Carlos Humberto Loitey, da sauran wasu manyan jami'an MDD, tare kuma da wakilan tawagogin kasashe daban-daban dake majalisar kusan dari uku sun halarci liyafar.

Shugaban kungiyar bada shawarwari ga ayyukan soja ta tawagar dindindin ta kasar Sin dake MDD, Hua Bo ya yi jawabi yana mai cewa, bana ake cika shekaru saba'in da MDD ta kaddamar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a duniya. Kuma tun da kasar Sin ta fara shiga ayyukan a shekara ta 1990, kawo yanzu, ta riga ta zama muhimmiyar kasa dake tura dakaru, gami da bada tallafin kudi ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.

Ya ce a shekara ta 2015, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi babban alkawari, a wajen taron kolin wanzar da zaman lafiya da MDD ta shirya, inda ya ce, kasarsa na goyon-bayan inganta ayyukan shimfida zaman lafiya na majalisar. Ya ce rundunonin sojan kasar Sin sun aiwatar da alkawarin da Xi ya yi, na nuna goyon-baya ga shawarwari da matakan da MDD ta dauka, ciki har da karfafa ayyukan wanzar da zaman lafiya, da tabbatar da tsaron dakaru masu shimfida zaman lafiya, da kuma kara jibge dakaru mata masu wannan aiki.

Mahalarta liyafar sun kuma nuna babban yabo ga ayyukan shimfida zaman lafiya da sojojin kasar Sin suka yi, gami da babbar gudummawar da suka bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China