Gwamnan jahar Durango Jose Aispuro ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa "Mun tabbatar da cewa ba'a samu hasarar rai ba a hadarin jirgin sama samfurin AM2431."
Ma'aikatar sufurin kasar tace jirgin saman mai daukar mutane 190 ya yi hadari ne jim kadan bayan ya tashi daga filin jirgin saman kasa da kasa na babban birnin jahar Durango.
Ministan sufurin kasar Gerardo Ruiz Esparza ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, jirgin yana dauke da fasinjoji 97 da kuma matukan jirgin 4.
Jirgin saman samfurin AM2431 yana kan hanyarsa ne ta zuwa birnin Mexico. (Ahmad Fagam)