in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Filin wasan kokawa na Senegal ya bude sabon babi na hadin kan Sin da kasar
2018-08-01 11:22:16 cri

A Senegal dake yammacin Afrika, dukkanin al'ummar kasar na kaunar wasan kokawa na gargajiya dake da tarihin fiye da shekaru dari. Idan akwai wata gasa mai muhimmanci, kowa da kowa na zuwa kallon wasan. Hakan ya sa wasan kokawa ya zama wata alama ta kasar. Amma kasar ba ta da wani fili mai kyau dake dacewa da wannan wasa, matsalar da ke ciwa wasan tuwo a kwarya.

Ranar 22 ga watan Yuli, Sin ta mikawa Senegal filin wasan kokawa wanda ya kasance alamar zumuncin dake tsakanin Sin da Senegal. Ginin na da fadin murabba'in mita dubu 18, wanda ke iya karbar masu kallo dubu 20, kana kuma ya kasance fili irinsa na zamani na farko a kasar.

Idan an shiga wannan fili, ana iya ganin abubuwan ado da aka yi da karafa masu tsawon mita 206.9, wanda sifarsu ta yi kama da wata damarar zinari, wanda ya yi nasara a gasar kokawa ke daurawa a kugu. Ban da wannan kuma, filin na da hawa na masu kallo har guda uku masu launukan ja, da rawaye da kore.

Ministan wasan motsa jiki na Senegal Matar BA ya ce, wannan fili dai ya cika mafarkin jama'ar Senegal a fannin wasan kokawa. Amma, wannan aiki mai muhimmanci ya fuskanci mawuyacin hali tun daga fara gina shi a shekarar 2016.

Mataimakin manajan kamfanin gine-gine na shida na CHCEG Mista Li Chao ya ce, wannan aiki ne ya kasance aikin da ba zai yiwu ba, saboda ganin wurin da aka zaba fadama ce dake cike da laka da ciyawa.

Tsakanin watan Yuli zuwa Oktoba, yanayin damina ne a Senegal, kuma ruwan sama a lokacin na haifar da wuya sosai ga masu aikin gini, hakan ya sa injuna dake dasa ginshikin ginin suke dasa ginshiki guda biyu kawai a kowace rana. Li Chao ya ce, hakan ya haifar masa da bacin rai sosai.

Amma abun mafi bata rai shi ne, sun fuskanci mawuyacin hali da dama ta fuskar harshe da bambamcin al'adu, abin da ya kawo cikas sosai ga aikinsa.

Duk da fuskantar wadannan mawuyacin hali, rukunin a karkashin Li Chao sun nuna himma da gwazo, sun dukufa cikin aiki ba tare da ja da baya ba ko kadan. Shugaban rukunin fasaha Xue Lichun, wanda ya yi aikin ba da taimako a kasashen waje har tsawo shekaru 15 ya ce, an gudanar da wannan aiki ne duka bisa shirin da aka tsara, don tabbatar ingancinsa.

Ban da wannan, kwararrun kasar Sin ba ma kawai sun ba da taimako kai tsaye a wurin aikin ba ne, har ma sun ba da horo ga 'yan Senegal da suka shiga wannan aiki, don kara karfinsu na sarrafa injuna da karfin aiwatarwa.

Mai aikin fasaha na Senegal dake da shekaru 53 a duniya Amadou Cisse, ya shiga wannan aiki ne tun daga shekarar 2016, ya sheda kafuwar wannan aiki daga farko zuwa karshe. Ya ce, yana farin ciki sosai da shigar sa wannan aiki, wanda 'yan Senegal suka dorawa muhimmanci sosai, horaswa da Sinawa suka bashi ta burge shi kwarai da gaske.

Hakazalika, yayin ake gudanar da wannan aiki, kamfanin ya gabatar da ayyuka na ba da tallafi ga wurin, don samarwa mazaunansa kayayyakin tallafi da kudi, ciki hadda shiga aikin gina manyan ababen more rayuwa, ba da taimako wajen share hanyar zuba ruwa, da gina filin wasan kwallon kafa, ayyukan dake samun karbuwa sosai daga jama'ar wurin.

Wannan filin wasan kokawa ya zama wata alama dake bayyana hadin kan Sin da Senegal wanda ya kara zurfafu. Ban da wannan fili, akwai gidan wasan kwaikwayon kasar, da gidan nune-nunen al'adun bakaken fata, da asibitin yara, da filin motsa jiki, wadannan ayyuka na bayyana makoma mai haske, ta bunkasuwar dangantakar Sin da Senegal. Kasashen biyu kuma sun kara fahimtar juna, da amincewa da juna, tare da cimma nasarori wajen hadin kansu.

Jakadan Sin dake Senegal Mista Zhang Xun ya ce, duk da cewa Sin da Senegal na da nisa sosai, amma ayyuka da dama da kasashen biyu suka yi cikin hadin kai sun kawo alfanu sosai ga mazauna wurin, kuma sun kulla hannaye da zukatan jama'ar kasashen biyu sosai. Ya yi imanin cewa, kasashen biyu za su kara hadin kansu, da kawo moriyar juna a fannoni daban-daban a nan gaba, don ba da gudunmawarsu wajen kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afrika, har ga dukkanin Bil Adam baki daya. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China