in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya zama jagoran ECOWAS na wannan karo
2018-08-01 10:14:29 cri
An zabi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ta ECOWAS. An zabi Buhari a taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar karo 53 da ya gabata a birnin Lome, fadar mulkin kasar Togo.

Buhari ya karbi ragamar jagorancin ECOWAS daga takwaransa na kasar Togo Faure Gnassingbe, biyowa bayan zaben da ya kasance daya daga cikin muhimman kudurorin taron na wannan karo.

Cikin jawabinsa na amincewa, shugaba Buhari ya alkawarta gudanar da ayyuka cikin hadin gwiwa da sauran takwarorinsa, ciki hadda wanzar da tsaro, da zaman lafiya, da mulki na gari, tare da tabbatar da kara raya ci gaban shiyyar yammacin Afirka, da daga matsayin kungiyar ta ECOWAS.

Ana fatan gudanar da taron kungiyar na gaba a ranar 21 ga watan Disambar karshen shekarar nan a Abuja fadar mulkin Najeriya. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China