in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Xi Jinping ta karawa al'umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afrika sabon karfin bunkasuwa
2018-07-31 11:28:28 cri

Watan Yuli, lokaci ne mai kyau a Afrika. Jama'ar Afrika na raye-raye da wake-wake don tarbar zuwan shugaba Xi nahiyar Afrika, tun daga kasar Senegal dake arewa maso yammacin Afrika zuwa kasar Rwanda, daga Afrika ta kudu dake kudancin Afrika zuwa Mauritius dake gabashin nahiyar, ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping ta samar da zarafi da sakwanni masu yakini, wajen kara hadin kan Sin da Afrika, da samun bunkasuwa, tare da bude sabon babi na dangantakar Sin da Afrika.

Ziyara ta farko ta wani shugaba na da ma'ana kwarai da gaske. Xi Jinping wanda ya lashe zaben zama shugaban kasar Sin a shekarar 2013, kana ya ci gaba da mulkinsa a bana, Afrika ta zama zango na farko na ziyararsa, matakin da ya bayyana zumuncin Sin da Afrika a wani matsayi mai muhimmanci. A cikin wadannan shekaru 5 da suka gabata, shugaba Xi ya taka nahiyar har sau 4, don zurfafa hadin kai da tsai da taswirar bunkasuwar bangarorin biyu mai yakini. Yana da niyyar raya hadin kan Sin da Afrika ta hanyar tuntunbar shugabannin bangarorin biyu, tare da gabatar da tunani da manufar bayyana sahihanci ga abokan Afrika, kuma ya daga dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika zuwa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkanin fannoni.

Ban da wannan kuma, yana kokarin inganta ginshigai mafiya muhimmanci biyar tsakaninsu, da gabatar da shirye-shiryen hadin kai guda 10 bisa tushen kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afrika, da zummar tsayar da taswirar bunkasa dangantakar Sin da Afrika cikin dogon lokaci.

Shirin kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afrika, na dogaro da bayyana juna sahihanci da zumunci. Sin da Afrika na da tarihi irin daya, suna da mafarin samun bunkasuwa bai daya. A cikin shekaru da dama da suka gabata, Sin da Afrika sun kulla hanayensu sun yi tafiya tare, dangantakar dake tsakaninsu na fuskantar sauye-sauye da dama, amma zumunci a tsakaninsu bai taba canjawa ba ko kadan. Har yanzu, Sin da Afrika na nace ga fahimtar juna, nunawa juna goyon baya. Tsoffi da sabbin shugabannin bangarorin biyu sun ci gaba da amincewa da juna da kara tuntubar juna, da kaiwa ga matsaya daya a siyasance, da zurfafa mu'ammala tsakanin jama'ar bangarorin biyu. Dukkanin matakan da suka burge zukatan jama'ar Afrika sosai.

Wannan shiri dai na dogaro ne da hadin kan Sin da Afrika da kawo moriyar juna. Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, muhimmin mataki dake cikin dangantakar bangarorin biyu shi ne bayyana sahihanci, wato bunkasa kasar Sin, don ba da taimako ga raya Afrika baki daya, har ma kawo moriyar juna da samun bunkasuwa tare.

Ba ma kawai Sin ta baiwa Afrika taimako kai tsaye ba ne, har ma tana ba da horo, kana ta gabatar da taimako ba tare da gindaya wani sharadi ba, da kuma kara hadin kai a fannin karfin kwadago, da musanyar fasaha da kimiya, kuma Sin ta nace ga inganta hadin kai, dangane da manyan ababen more rayuwa, da yankuna na musamman na tattalin arziki, da yankunan masana'antu, don taimakawa Afrika ta jawo karin jari daga kasashen waje.

A halin yanzu, Afrika na kokarin tabbatar da masana'antu na zamani, Sin kuma tana dukufa kan sa kaimi ga garabawul kan tsarin tattalin arziki, da kyautata hanyar samun bunkasuwa, matakin da ya sa bangarorin biyu ke fuskantar zarafi mai kyau na hada kansu. A ziyarar shugaba Xi a wannan karo, ya kulla yarjeniyoyi fiye da 40 na hadin kan Sin da Afrika, ciki hadda yarjejeniyar dake shafar shawarar "Ziri daya da hanya daya", matakin da ya samar da wani sabon dandali, da inganta hadin kan bangarorin biyu.

Zumuncin Sin da Afrika na da sahihanci sosai, kuma suna hadin kai mai inganci. Kasashen Afrika suna da fahimta sosai kan hakikkanin hadin kan Sin da Afrika. Yayin ziyarar Xi Jinping da wasu shugabannin Afrika, shugabannin sun bayyana matsayinsu na rashin jin dadi game da ra'ayin sabon manufar mulkin mallaka, kuma kuna sa ran hadin kai Sin da Afrika zai samu ci gaba mai armashi.

Layin dogo dake tsakanin Mambasa da Nairobi, a matsayin daya daga cikin wasu manyan ayyuka dake cikin shawarar "Ziri daya da hanya daya" ya fara aiki a watan Yuni na bana, wanda ya kai ga safarar fasinjoji har miliyan 1.35, ya ba da taimako sosai ga zirga-zirgar a wurin. Ban da wannan kuma, tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa da Sin ta ba da taimako wajen gina ta, ta warware matsalar karancin makamashi a wasu kasashen Afrika, har ma gwamnatin Guinea ta buga hoton tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa da Sin da Afrika suka gina cikin hadin kai, kan kudin takardarta domin tunawar da kai muhimmancin aikin.

Ci gaba mai armashi da Sin da Afrika suka samu cikin hadin kai, na baiwa jama'ar bangarorin biyu kwarin gwiwa game da nan gaba. Aminai Sin da Afrika kamar kawaye ne da za su iya cimma mafarkinsu cikin hadin kai nan gaba.

A cikin watan Satumba, za a kira taron koli na birnin Beijing na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika. Muna sa ran taro mai taken "Hadin kai da cimma muradun juna, da kafa wata al'umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afrika" zai haifar da ci gaba, ya kuma kai ga cimma matsaya da dama. Alamar dandalin ita ce ban hannu da ake yi, na bayyana hadin kan Sin da Afrika, da samun bunkasuwa da makomar Bil Adam a nan gaba tare. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China