in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Algeria ta amince da tuso keyar mutane 727 a cikin shekaru 3
2018-07-31 10:45:15 cri
A tsakanin shekaru 3 na baya bayan nan, mahukuntan kasar Algeria sun amince da cafke mutane 727, bisa zargi su da aikata muggan laifuka da suka keta dokokin kasa da kasa.

Ministan shari'ar kasar Tayeb Louh ne ya bayyana hakan a jiya Litinin, yayin da yake jawabi a wata kwalajin koyar da harkokin shari'a dake lardin Tipasa, mai nisan kilomita 40 yamma da birnin Algiers.

Louh ya ce tsakanin watan Yulin shekarar 2015 zuwa Yulin bana, Algeria ta ba da umarnin kama mutane 727 daga kasashen ketare, bisa zargin su da aikata muggan laifuka, an kuma fara gudanar da matakai na tiso keyar su zuwa kasar domin su fuskanci shari'a.

Kaza lika a cewar jami'in, tsare tsaren da ake bi na cikin manufofin kasashen arewacin Afirka, na yaki da laifukan da suka shafi kan iyakokin su, wadanda ke barazana ga dinkewar al'ummun shiyyar.

Hakan a cewar sa na zuwa ne, yayin da zirga zirgar al'ummu ke karuwa, kana batun kwararar 'yan ci rani ke kara zama ruwan dare, kuma ayyukan ta'addanci da na masu safarar miyagun kwayoyi ke kara bazuwa.

Mr. Louh ya ce Algeria ta sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama tsakanin ta da kasashe da wasu hukumomin shari'a, wadanda suka jibanci tusa keyar masu laifi zuwa kasashen su, domin cimma nasarar yakin da ake yi da muggan laifuka dake wakana a shiyyar ta. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China