Li Keqiang ya bayyana haka ne yayin taron majalisar gudanarwar kasar Sin da ya gudana a jiya, bayan ya saurari rahoton ayarin majalisar da ya yi karin haske kan kura-kuran da kamfanin Changchun Changsheng Life Science Limited ke tafkawa wajen hada riga kafin cutar haukar kare domin amfanin bil adama.
Sanarwar da aka fitar bayan taron, ta ce masu bincike sun gano cewa, kamfanin ya karya ka'idoji sosai, inda ya yi sauye-sauye cikin tsarin hada riga kafin da samar da rahoton ayyukan da na sa ido na bogi tare da lalata wasu shaidu.
Ta ce 'yan sanda sun nemi izinin kama wadanda ake zargin na da hannu cikin aikin samar da riga kafin.
Har ila yau, sanarwar ta ce za a yankewa wadanda ke da alhakin aikata laifin hukunci mai tsauri tare da tara mai yawa, yayin za a tura wadanda suka aikata manyan laifi zuwa gidan kaso da kuma haramta musu aiki a bangaren samar da magunguna har abada. (Fa'iza Mustapha)