Wata sanarwa da hukumar ta CCDI ta fitar a jiya Litinin ta bayyana cewa, laifukan da jami'an suka aikata sun shafi harkokin aiki 25,677, wadanda mafi yawansu suka shafi biyan alawus alawus, da kudaden gatanci na aiki ba tare da bin ka'idojin da doka ta tanada ba. Sai kuma bayarwa, da karbar kyaututtuka, da amfani da ababen hawa na gwamnati ba bisa ka'ida ba.
Hukumar ta CCDI ta ce a watan Yunin da ya gabata, ta hukunta jami'ai 9,519 bisa aikata laifuka 6,692. A karshen shekarar 2012 ne dai JKS ta fidda wasu ayoyin doka 8, wadanda suka tanaji matakan dakile karya dokoki ta hanyar amfani da gudummawar al'umma, a yakin da ake yi da karya dokoki da tsimin kudade.
Hukumar CCDI na fidda rahotannin aikin ta a duk wata, wanda ke kunshe da matakan tsuke bakin aljihu a matakai na larduna, da kwamitin kolin jam'iyya, da na hukumomin gwamnati daban daban, da ma hukumomi da cibiyoyin hada hadar kudade. (Saminu Alhassan)