in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD na tattauna yiwuwar dagewa Eritrea takunkumi
2018-07-31 09:39:05 cri
Kwamitin tsaron MDD na tattauna yiwuwar dagewa kasar Eritrea takunkumi sakamakon wasu sauye sauye da kasar ke aiwatarwa.

Da yaka bayyana hakan, wakilin kasar Sweden a MDD, wanda kuma kasar sa ke jagorantar kwamitin tsaron a watan nan na Yuli Mr. Olof Skoog, ya ce kwamitin yayi maraba da matakan da kasashen Eritrea da Habasha ke dauka a baya bayan nan, game da inganta tsaro da warware takaddamar su.

Skoog wanda ya zanta da manema labarai, bayan wani zaman sirri da mambobin kwamitin na tsaro suka gudanar game da Eritrea da Habasha, ya jaddada aniyar kwamitin na tsaro, wajen tallafawa kyautatuwar yanayin tsaro a yankin na kahon Afirka.

Da yake amsa tambaya game da yiwuwar dagewa Eritrea takunkumi, Skoog ya ce an tattauna game da hakan, kuma a madadin kwamitin na tsaro, yana mai alkawarta burin su na goyawa yunkurin wanzar da zaman lafiya a shiyyar baya.

Habasha dai ta bukaci kwamitin tsaron MDD ya dagewa Eritrea takunkumi, bayan da kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da kawance a ranar 9 ga watan Yulin nan. Kaza lika Habasha ta bayyana aniyarta ta tallafawa Eritrea da Djibouti, da matakan warware rikicin kan iyaka da suka dade suna fama da shi, tare da tabbatar da kyautatuwar dangantaka tsakanin sassan biyu.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China