in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Peter Kagwanja: Aikin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare da kasar Sin ke yi ya kawo wa kasashen Afirka damar neman ci gaba
2018-07-30 11:59:18 cri

A shekarar 1978, an samu wani muhimmin sauyi mai ma'ana matuka a tarihin kasar Sin, wato a wannan shekara, an shirya cikakken zama na 3 na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 11, inda aka sa niyyar aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida, tare kuma da bude kofar kasar Sin ga ketare. Lalle, manufar ta bude wani sabon shafi ga ci gaban kasar Sin. A wancan lokaci, yawancin kasashen Afirka wadanda suke da nisa sosai da kasar Sin sun samu 'yancin kai daga mulkin mallaka, sun kuma shiga wani muhimmin lokacin neman ci gaba. Kawo yanzu, shekaru 40 ke nan da kasar Sin ta kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare. Wadannan ci gaban da kasar Sin ta samu a fannonin tattalin arziki da zaman takewar al'umma a cikin wadannan shekaru 40 da suka wuce, ya kawo sauye-sauye sosai ga zaman rayuwar al'ummar kasar, har ma ya kasance tamkar wani karfin neman ci gaba ne ga kasashen Afirka wadanda su kan maida hankali kan yadda kasar Sin take samun ci gaba.

A lokacin zafi na wata rana da yamma a shekarar 1972, a wata makarantar firamaren kasar Kenya, a karo na farko Peter Kagwanja, dalibi mai shekaru 9 da haihuwa ya san kogin Rawaye na kasar Sin. Bayan shekaru 40, a matsayin shugaban cibiyar nazarin manufofin kasashen Afirka, kana mamba mai bada shawarwari kan dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, cikin jirgin kasa mai saurin tafiya da ya tashi daga birnin Beijing, Peter Kagwanja ya ga wannan kogin Rawaye da idonsa, nan da nan ya dauki hoto ya sanya wannan kogin a kan fim nasa.

A shekarar 1960, adadin cinikayyar da aka yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ya kai dalar Amurka miliya dari 1 kawai a duk shekarar. Bayan da kasar Sin ta kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare a shekarar 1978, adadin cinikayyar da aka yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ya kai dalar Amurka biliyan 1 a shekarar 1980. Dalibi Peter Kagwanja wanda yake karatu a wata makarantar sakandare ya gano cewa, yawan kayayyaki kirar kasar Sin da za a iya zaba ya karu. A lokacin da yake tunawa da wancan lokaci, Mr. Peter Kagwanja ya bayyana cewa, daga farkon lokacin kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, kasar Sin ta kawowa al'ummomin Afirka sakamakon a zo a gani. Mr. Peter Kagwanja ya ce, "A farkon lokacin da kasar Sin ta kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, ya yi gwajin bunkasa tattalin arzikinta bisa bukatun da ake da su a kasuwa, sannan ta soma rungumar kasuwannin kasashen duniya sannu a hankali. Al'ummomin Afirka suna farin ciki sosai sabo da sun gano wannan tarihi. Karin kayayyaki kirar kasar Sin masu inganci kuma masu araha sun shiga kasuwannin kasashen Afirka, ciki har da murhu da kayayyakin karatu na dalibai da kayayyakin aikin gona wadanda suke daidai da karfin sayensu na al'ummomin Afirka wadanda suke cin gajiyar wannan manufar da kasar Sin ta aiwatar."

Bayan an shiga sabon karni, kasar Sin ta aiwatar da manufar zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare. Hakan ya sa ta zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duk fadin duniya. Mr. Peter Kagwanja ya bayyana cewa, a lokacin da kasar Sin take kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare, tana nuna hakurinta sosai da bambancin dake kasancewa tsakaninta da sauran kasashen duniya, musamman shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, ta kawowa sauran kasashen duniya, ciki har da kasashen Afirka karin damammakin neman ci gaba.

"Ba ma kawai kasar Sin ita kanta tana cin gajiyar manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare ba ne, har ma ta taimakawa kasashen Afirka wajen hanzarta bude kofarsu ga ketare. Shawarar 'ziri daya da hanya daya' da kasar Sin ta gabatar ta tabbatar da wannan batu. Alal misali, layin dogo da kasar Kenya ta shimfida bisa tallafin kasar Sin tsakanin Nairobi da Mombasa ya karfafa mu'amala tsakanin yankunan dake bakin teku da sauran yankunan dake nesa da teku na kasar Kenya, har ma da sauran yankunan gabashin Afirka."

Bunkasa masana'antu da inganta karfinsu na neman ci gaba da kansu su ne babban burin da yawancin kasashen Afirka suke son cimmawa. Peter Kagwanja ya ce, a kullum kasar Sin na nuna goyon baya bisa karfinta ga kasashen Afirka da su nemi ci gaba bisa karfinsu.

Mr. Peter Kagwanja ya kawo ziyarce-ziyarce kasar Sin sau da dama. Jirgin kasa mai saurin tafiya da yake gudun kilomita dari 3 a kowace sa'a, da yadda karamin kauye na lardin Hunan ya samu sauye-sauye sosai, dukkansu sun zama misalan dake bayyana yadda kasar Sin take samun sakamakon a zo a gani bayan da ta kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare. Amma abin da ya fi burge Peter Kagwanja shi ne tunanin neman ci gaban tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba da kasar Sin take aiwatarwa yanzu. Mr. Peter Kagwanja ya ce, wannan tunani ya kai kasashen Afirka su yi koyi da shi.

"A 'yan shekarun baya baya nan, tunanin kare muhalli, musamman aikin dasa bishiyoyi da kasar Sin ta yi ya burge ni kwarai da gaske. A lokacin da nake birnin Shanghai, na bude taga, bishiyoyi sun cika idona, ina gamsu da yanayin. A ganina, ya kamata kasashen Afirka su yi koyi da wannan fasahar neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli da kasar Sin ta samu." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China