in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta karfafa baiwa kayan tarihi masu nasaba da juyin juya halin kasar kariya
2018-07-30 10:41:13 cri
Kasar Sin ta fitar da wasu manufofi, na baiwa kayan tarihi masu nasaba da juyin juya halin kasar kariya ta musamman, a wani mataki na adana irin wadannan kayayyaki da wurare.

Mahukuntan kasar sun dauki wannan mataki ne dai da nufi bunkasa manufofin kishin kasa, tare da kara gina burin kasar Sin na samun cikakkiyar farfadowa a zukatun al'ummar ta.

Bisa tsarin aiwatar da hakan, wanda ofisoshin kwamitocin koli na JKS, da na majalissar zartaswar kasar suka fitar, an umarci sassan dake da nauyin yayata manufofin kasa da na al'adu a matakan larduna, su gudanar da cikakken nazari, game da wurare ko abubuwan da suka faru na al'adu masu nasaba da juyin juya halin kasar ta Sin, domin gabatar da su ga jama'a.

Kaza lika ana fatan tsakanin shekaru 2018 zuwa 2022, za a farfado da dukkanin wuraren tarihi masu nasaba da kafuwar JKS, ta yadda hakan zai tallafa wajen karfafa ba da kariya da aiwatar da manufofin raya al'adu masu nasaba da juyin juya halin kasar, da gadar da su ga zuriya ta gaba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China