in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasuwar kasar Sin dama ce da bai kamata kasashen duniya su rasa ba
2018-07-28 20:39:19 cri
Nan da kwanaki dari, za'a kaddamar da bikin baje-kolin kasa da kasa karo na farko, kan kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga ketare, a birnin Shanghai. Kawo yanzu, akwai kamfanoni fiye da 2,800 daga kasashe da yankuna sama da 130 da suka yi rajistar halartar bikin, kana, bisa hasashen da aka yi, akwai masu sayayya kimanin dubu 150 daga duk fadin duniya wadanda za su halarta.

Kamfanonin da suka fi yin rajistar halartar bikin kamfanoni ne masu sarrafa tufafi da kayayyakin yau da kullum da abinci da kuma amfanin gona, a yayin da kamfanonin sarrafa na'urorin zamani da motoci suka fi neman fadin filinsu a wajen bikin. A zahiri dai, yadda Sinawa ke neman ingancin rayuwa da na ci gaban tattalin arziki, sun zama abin da ke sa kaimin karuwar kasuwar duniya.

Dalilin da ya sa bikin baje-kolin da gwamnatin kasar Sin za ta shirya ya jawo hankalin duniya sosai shi ne, yayin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar kalubale sakamakon matakan da wasu kasashe ke dauka na bada kariya ga harkokin kasuwanci, kamfanoni da dama na fatan kawar da tsaikon, da lalubo sabuwar hanyar samun riba. Sin kasa ce dake da mutane kusan biliyan 1.4 da babbar kasuwar zuba jari, haka kuma gwamnatinta na goyon-bayan cinikayya cikin 'yanci, da kawo sauki ga harkokin zuba jari, da kuma kara bude kofa ga kasashen waje. Don haka Sin ta zama kyakkyawar dama ga sauran kasashen duniya.

Yanzu Sin ta zama kasa mafi girma a duniya dake shigo da amfanin gona daga sauran kasashe gami da cinikin motoci. Ahalin yanzu, masu matsakaicin kudin shiga sun kai kimanin miliyan 400 a kasar Sin. A cikin 'yan shekarun baya, naman sa da aka shigo da shi daga kasar Australia da 'ya'yan itatuwan cherry na kasar Chile da kuma madarar kasar Jamus da ma sauran amfanin gona masu inganci na kasashen ketare na kara fitowa a teburin cin abincin al'ummar kasar Sin. Kasar Sin ta zamanto kasar da ta fi shigo da amfanin gona daga kasashen duniya, har ma yawan amfanin gona da take shigowa daga ketare ya dau kaso 10% na yawan amfanin gona da ake cinikinsu a duniya baki daya, kuma gibin kudin ciniki a wannan fanni ya kai kimanin dala biliyan 40 zuwa 50 a gare ta a kowace shekara. A ganin jaridar Financial Times ta kasar Burtaniya, galibin masana'antun sarrafa motoci na kasa da kasa na samun a kalla rubu'in ribarsu ne daga kasar Sin. A ranar 1 ga watan Yulin wannan shekara, a hukumance, kasar Sin ta rage kudin haraji kan motoci da ma wasu kayayyakin yau da kullum da take shigowa da su daga kasashen waje, matakin da ya biya bukatun masu sayayya na kasar, tare kuma da samar da karin moriya ga kamfanonin kasashen waje da ke neman kasuwar kasar Sin.

Kasancewarta kasa daya kacal a duniya da ke da dukkanin nau'o'in masana'antu da ke cikin takardar jerin nau'o'in masana'antu da MDD ta tsara, kasar Sin tana kuma kara bude kofarta ga jarin waje. A karshen watan Yuni, kasar Sin ta fitar da gyararriyar takardar matakan kayyade fannonin da 'yan kasuwar kasashen ketare ke iya zuba jari, inda ta kara bude kofarta ta fannonin hada-hadar kudi da manyan ayyuka da sufuri da al'adu da motoci da jiragen ruwa da jiragen sama da noma da makamashi da albarkatun kasa da sauransu, har ma ta kai ga rage kusan kashi daya daga cikin hudu na matakanta na kayyadewa. Babu shakka wannan zai kara karfafa gwiwar masu zuba jari na kasashen waje.

Ban da wannan, kasar Sin na da tushe mai inganci na raya tattalin arziki, haka kuma tana kokarin kyautata yanayin cinikayya, gami da yin kirkire-kirkire ga manufofin neman ci gaba, al'amuran da suka sa ta zama kasa dake jan hankalin masu zuba jari matuka daga fadin duniya. A farkon rabin shekarar 2018, tattalin arzikin kasar Sin ya karu da kaso 6.8% bisa makamancin lokacin a bara, kuma kungiyar hadin kan tattalin arziki da bankin raya kasashen Asiya sun daidaita hasashensu kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a wannan shekara da karin kashi 0.1% da kuma 0.2%.

A halin yanzu, ana kokarin yin sabbin sauye-sauye ga masana'antu da fasahohi a duk fadin duniya baki daya. Baya ga wasu sana'o'in gargajiya, yawan kamfanonin dake yin kirkire-kirkire a kasar Sin ya zama na biyu a duniya, inda a karon farko ta shiga jerin kasashe 20 dake kan gaba a duniya wajen yin kirkire-kirkire bisa mizanin kungiyar kare ikon mallakar fasaha ta duniya. Har wa yau, sakamakon matukar kokarin da kasar Sin ke yi a fannonin makamashi mai tsabta, da motoci masu amfani, da wutar lantarki, da batir da sauransu, za'a yi hasashen cewa, jari gami da kamfanonin kasashen waje za su kara samun bunkasuwa a kasar ta Sin.

A bana ake cika shekaru 40, tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje. A baya bayan nan, a wajen taron dandalin tattaunawa kan harkokin masana'antu da kasuwanci tsakanin kasashen BRICS wanda aka yi a kasar Afirka ta Kudu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi, inda ya sake jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da bude kofarta ga kasashen waje, da fadada kayayyakin da take shigowa da su daga kasashen ketare, da kara kokarin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", don samar da sabbin damammaki ga sauran kasashe wajen neman ci gaba.

Bisa shirin da shugaba Xi ya sanar a wajen dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya wanda aka yi a Davos a bara, daga shekara ta 2017 zuwa ta 2021, kasar Sin za ta shigo da kayayyakin da darajarsu ta kai dala triliyan 8, da jawo jarin waje da yawansa ya kai dala biliyan dari shida, kuma yawan jarin da Sin za ta zuba a kasashen waje zai kai dala biliyan 750. Ko shakka babu, bikin baje-kolin kasa da kasa na farko, kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje, da za'a yi a birnin Shanghai zai samar da dandali mai muhimmancin gaske ga 'yan kasuwan kasashen waje, ta yadda za su shiga cikin kasuwannin kasar Sin kai-tsaye. Kasar Sin babbar kasuwa ce da bai kamata masu zuba jari na kasashen waje su rasa ba wajen samun riba.(Murtala Zhang, Lubabatu Lei)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China