Guterres wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ta hannun kakakinsa Stephane Dujarric, ya kuma aike da sakon ta'aziya ga gwamnati da al'ummar Pakistan da ma iyalan wadanda harin ya rutsa da su. Ya kuma ce MDD tana goyon bayan matakan da mahukuntan Pakistan ke dauka kan yaki da ayyukan ta'addanci.
Koda a tsakiyar watan Yulin wannan shekara ma, mutane 149 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kaddamar yayin gagamin yakin neman zabe a garin Mastung dake lardin na Balochistan. Ana zargin kungiyar IS da kaddamar da hare-haren. (Ibrahim Yaya)